NNPP: Jam'iyyar Kwankwaso Ta Dakatar da Dan Takarar Gwamna da Mataimakinsa
- Jam’iyyar NNPP a Ondo ta dakatar da tsohon dan takarar gwamna, Olugbenga Edema da mataimakinsa Rotimi Adeyemi
- Shugaban NNPP na Ondo, Peter Olagookun, da wasu jiga-jigan jam’iyyar 12 ne suka sanya hannu kan takardar dakatarwar
- An ce Edema ya kai jam’iyyar kotu ba tare da tuntubar shugabanni ba, ya kuma shiga harkokin da ke cin amanar NNPP
- Edema ya fadi zaben gwamnan Ondo, amma kafin haka ya kai karar APC yana bukatar INEC ta soke takarar Aiyedatiwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Akure, Ondo - Jam’iyyar NNPP a Ondo ta dakatar wanda ya yi mata takarar gwamna a zaben 2024 da aka gudanar.
Jam'iyyar NNPP ta dakatar da Olugbenga Edema, da mataimakinsa, Rotimi Adeyemi, ba tare da wa’adin dawowa ba kam wasu zarge-zarge masu girma.

Asali: Facebook
An dakatar da dan takarar gwamna a NNPP
Wannan na kunshe ne a cikin wata wasika mai kwanan wata 3 ga Maris din 2025 da shugabannin jam'iyyar suka sanya wa hannu, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Edema ya fadi zaben gwamna da aka yi a ranar 16 ga Nuwambar 2024, inda Lucky Aiyedatiwa na jam’iyyar APC ya kayar da shi a zaben.
Kafin zaben, Edema ya kai kara a kotun tarayya da ke Akure yana neman soke takarar Aiyedatiwa da kuma hana INEC amincewa da shi.
Ya ce Aiyedatiwa da mataimakinsa sun ci zaben fidda gwani ne ta hanyar da ba ta dace ba, wanda ya saba wa tanadin dokar zabe ta 2022.
NNPP ta kuma dakatar da wani mamba, Israel Ayeni, bisa zargin cin amanar jam’iyya da karya dokokinta.

Asali: Facebook
Musabbabin dakatar da Edema daga jam'iyyar NNPP
Shugaban NNPP a Ondo, Peter Olagookun, tare da wasu jiga-jigan jam’iyya 12, ne suka sanya hannu kan takardar dakatarwar da ta shafi ‘yan siyasar uku a jihar baki daya, Tribune ta ruwaito.
Olagookun ya ce an dakatar da su ne saboda:
"Shigar da kara a madadin jam’iyya ba tare da tuntubar shugabanni a matakin jiha da na kasa ba wanda ya saba doka kuma hakan cin amanarta ne."
Ya kara da cewa:
“Shigar da kara ba tare da bin hanyoyin sulhu na cikin gida kamar yadda dokokin jam’iyya suka tanada ba, da shiga cin amanar jam’iyya.”
Wannan lamari ya kara jefe jam'iyyar ta NNPP a tsakiyar rigingimun cikin gida.
Edema ya koma NNPP ana daf da zabe
A baya, kun ji cewa Barista Olugbenga Edema ya zama ɗan takarar gwamnan Ondo a karkashin NNPP bayan ya baro jam'iyyar APC da ke mulkin jihar.
Tsohon jigon jam'iyya mai mulki ya ce ya shirya sauke Gwamna Lucky Aiyedatiwa daga mulki a zaɓen watan Nuwambar 2024 wanda daga bisani ya sha kaye da mummunan rata.
Jam'iyyar NNPP ta ba Edema tikitin takara ne bayan tsohon ɗan takararta, Oluwatosin ya janye daga takara bisa ra'ayin kansa da kishin tsantsar kishin jam'iyya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng