Tinubu Ya Yi Magana kan Saukar Farashin Abinci, Ya Yi Alkawarin Karin Sauki

Tinubu Ya Yi Magana kan Saukar Farashin Abinci, Ya Yi Alkawarin Karin Sauki

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu goyon baya daga kwamitin zartaswa na APC yayin taron da jam’iyyar ta yi a Abuja
  • Tinubu ya ce yana aiki tukuru don tabbatar da ci gaban tattalin arzikin Najeriya tare da yin farin ciki kan saukar farashin abinci
  • Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta fi maida hankali kan bunkasa harkar abinci, zuba jari, da ci gaban kasa ta fannoni dadan daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya samu cikakken goyon baya daga kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC a wani taro da aka gudanar a Abuja.

A yayin taron, Tinubu ya yi alkawarin kara himma domin tabbatar da ci gaban Najeriya da inganta rayuwar al’ummar kasar nan.

Kara karanta wannan

APC ta fadi abin da zai mayar da Tinubu kujerarsa bayan zaben 2027

Bola Tinubu
Tinubu ya yi farinci da saukar farashi. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Hadimin shugaban kasa, Dada Olusegun ya wallafa a X cewa shugaba Tinubu ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya yana kan hanyar farfadowa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka, Tinubu ya ce zai ci gaba da yin aiki tukuru domin inganta harkokin kasuwanci da walwalar jama’a.

Bola Tinubu ya samu goyon bayan APC

Shugaba Tinubu ya nuna farin cikinsa bisa yadda manyan shugabannin jam’iyyar APC suka nuna goyon baya ga gwamnatinsa.

Ya bayyana hakan ne a yayin taron kwamitin zartaswa na APC, inda ya ce goyon bayan da ya samu ya kara masa karfin gwiwa domin cigaba da kokari.

"Ina matukar godiya da goyon bayan da kuka nuna mini, hakan ya zama babban kalubale a gare ni domin kara kokari.
"Za mu ci gaba da kokarin tabbatar da wadatar abinci, zuba jari, da ci gaban kasa,"

Maganar Tinubu kan saukar farashin abinci

Tinubu ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya yana habaka a hankali, kuma farashin kayan abinci na raguwa musamman yayin da watan Ramadan ke karatowa.

Kara karanta wannan

Bayan kusoshin APC sun kaurace wa taron jam'iyya, Tinubu ya dora wa Ganduje aiki

Shugaban kasar ya ce:

"Ina farin ciki da yadda ake samun saukin farashin abinci, musamman da Ramadan ke tafe.
"Najeriya tana samun cigaba yayin da sauran kasashe ke fuskantar kalubale. Mun ga alamu na dawowar zaman lafiya da ci gaban kasa."

Ya kuma gode wa ‘yan Najeriya bisa yadda suka ci gaba da ba APC goyon baya, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da sauran bangarorin gwamnati

Tinubu ya yaba da aikin gwamnonin APC

Shugaban kasar ya jinjinawa gwamnonin jam’iyyar APC da sauran jiga-jigai bisa kokarin da suke yi wajen cigaban jam’iyyar.

"Ina godiya ga gwamnoninmu da shugabannin jam’iyya da suka rungumi sauye-sauyen da muke kokarin kawowa.
"Ina kuma godewa ‘yan majalisa bisa yadda suka gaggauta amincewa da kasafin kudi,"

- Bola Tinubu

Tinubu
Tinubu da jiga jigan APC yayin taro a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Bukatar warware rikicin APC a jihohi

Shugaba Tinubu ya yaba da yadda kwamitin gudanarwa na APC ke tafiyar da jam’iyyar, amma ya bukaci a dauki matakin magance wasu rikice-rikicen siyasa da ke faruwa a jihohi.

Kara karanta wannan

A gaban Tinubu da manyan jiga jigai, Ganduje ya bankado abubuwan da ya tarar a APC

"Kwamitin gudanarwa yana aiki tukuru, kuma ina matukar jin dadin hakan. Sai dai akwai wasu rikice-rikice a jihohi daban-daban.
"Ina kira da a kafa kwamitoci da za su duba matsalolin da ke tasowa a jihohi kuma su sasanta shugabannin jam’iyyar don a samu zaman lafiya,"

- Bola Tinubu

Tinubu ya yi magana kan tallafin mai

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa matakin da ya dauka kan cire tallafin man fetur yana kan daidai.

Tinubu ya ce matakin ya zama dole duk da wahalar da ake sha na kankanin lokaci, ya ce da ba a cire tallafin ba, da Najeriya za ta iya durkushewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng