Buhari Ya Kare Kansa bayan Ya Ki Halartar Babban Taron Jam'iyyar APC
- Tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Muhammadu Buhari ya ƙi halartar babban taron jam'iyyar APC da aka yi a Abuja
- Hakazalika manyan ƙusoshin APC da suka haɗa da Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi da Kayode Fayemi ba su je ba
- Hadimin shugaba Buhari ya bayyana cewa duk da bai halarci taron ba, har yanzu zuciyarsa na tare da jam'iyyar APC
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bai samu halartar babban taron jam'iyyar APC da aka shirya a yau ba.
Hakazalika akwai manyan ƙusoshin jam'iyyar APC waɗanda aka kafa jam'iyyar da su, da ba a gansu ba a wajen taron na ranar Laraba.

Asali: Facebook
Jaridar The Sun ta ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo na daga cikin waɗanda suka ƙi zuwa wajen babban taron.

Kara karanta wannan
A gaban Tinubu da manyan jiga jigai, Ganduje ya bankado abubuwan da ya tarar a APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu dai da sauran jigan-jigan jam'iyyar APC sun halarci taron wanda ake gudanarwa a sakatariyar APC ta ƙasa da ke Abuja.
Wasu ƙusoshin APC ba su halarci taro ba
Sauran ƙusoshin APC da ba su halarci taron ba sun haɗa da tsofaffin gwamnoni irin su Malam Nasir El-Rufai na Kaduna, Rotimi Amaechi na Rivers da Kayode Fayemi na jihar Ekiti.
Hakalika tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan da tsohon shugaban majalisar wakilai kuma shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ba su halarci taron ba.
Rashin ganinsu a wajen babban taron na APC ya sanya alamar tambaya domin ya kamata a ce sun halarci zaman.
Babu dai wani dalili da ya fito fili kan rashin halartar manyan ƙusoshin na jam'iyyar APC.
Meyasa Buhari bai halarci taron APC ba?
Tashar BBC Hausa ta rahoto cewa tsohon hadimin Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya bayyana dalilin rashin ganin tsohon shugaban ƙasan a wajen taron.

Kara karanta wannan
Tsohon shugaba Buhari, El-Rufa'i da sauran jagororin APC sun ki halartar taron APC
Garba Shehu ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasan ba shi daga cikin mambobin majalisar ƙoli ta jam'iyyar APC.
Tsohon hadimin na Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk da tsohon shugaban ƙasar bai halarci taron ba, zuciyarsa tana tare da APC domin ta yi masa gata.
"Shugaba Buhari ba shi daga cikin mambobin majalisar ƙolin jam'iyyar APC. Taron masu ruwa da tsaki wanda aka yi ranar Talata ya kamata a ce ya halarta."
"Abin da ya sa ba a gan shi a taron na ranar Talata ba, shi ne sai a ranar Litinin aka aika masa da wasiƙar gayyata, amma ba ta tarar da shi ba sai ranar Talata da rana."
"Ka ga ai ba zai iya barin Daura har ya je Abuja ya halarci taron ba ko da kuwa yana da jirgin kansa."
- Malam Garba Shehu
El-Rufai ya faɗi tasirin Buhari a siyasarsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana rawar da Muhammadu Buhari ya taka a wajen zamansa gwamna.
Nasir El-Rufai ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasan ne ya sanya shi tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna a zaɓen 2015.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng