A gaban Tinubu da Manyan Jiga Jigai, Ganduje Ya Bankaɗo Abubuwan da Ya Tarar a APC
- Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ya gaji bashin sama da Naira biliyan 8 a lokacin da ya karɓi shugabancin jam'iyyar APC mai mulki
- Ganduje ya faɗi tulin bashin da ya yi wa APC katutu ne a taron kwamitin zartarwa watau NEC wanda ke gudana yau Laraba a birnin tarayya na Abuja
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, mataimaikinsa Kashim Shettima da manyan kusoshin APC a matakin ƙasa da jihohi sun halarci wannan taro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana tulin bashin da ya tarar a jam'iyya mai mulki lokaci da ya karɓi shugabanci.
Ganduje ya ce kwamitin gudanarwa na APC ta ƙasa (NWC) wanda yake jagoranta ya gaji bashin N8,987,874,663 lokacin da suka karbi ragamar jam'iyya.

Asali: Facebook
Tsohon gwamnan jihar Kano ya yi wannan bayani ne a taron kwamitin zartaswa na kasa (NEC) wanda ke gudana a sakateriyar APC da ke Abuja, rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya halarci taron NEC
Taron ya samu halartar manyan ƙusoshin jam'iyya mai mulki ciki har shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Sanata Kashim Shettima.
Sauran waɗanda suka halarci taron na yau Laraba, 26 ga watan Fabrairu, 2025 sun kunshi shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas.
Haka zalika gwamnonin jihohin da APC ke mulki, ƴan kwamitin NWC, da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar a matakin ƙasa da jihohi duk sun halarci taron.
Ganduje ya gaji bashin N8.9bn a APC
Da yake jawabi a gaban Tinubu da sauran kusoshin APC, Ganduje ya bayyana cewa basussukan da ya gada suna da nasaba da shari’o’in da ke gudana a gaban kotu.
Shugaban APC na ƙasa ya ƙara da cewa galibin shari'o'in sun shafi zabuka daban-dabam da aka yi tun kafin ya karɓi shugabancin jam'iyya.
A rahoton Daily Trust, Ganduje ya ce:
“Kwamitin NWC ya gaji bashin Naira biliyan 8.9 wanda ya samo asali daga shari’o’i daban-daban da suka shafi zabuka, ciki har da na zaɓukan ƴan majalisu, gwamnoni, da na shugaban kasa.”
Shugaban APC ya nemi tallafin NEC
Sai dai ya kara da cewa lauyan jam’iyyar na kasa, Farfesa Abdul Kareem Kana (SAN), yana kokarin rage nauyin bashin ta hanyar tattaunawa da amfani da hanyoyin warware matsaloli ba tare da shari’a ba.
Ganduje ya bukaci tallafin kwamitin NEC, yana mai cewa wasu daga cikin asusun ajiyar jam’iyyar har yanzu suna kulle saboda basussuka.
Tsohon gwamnan ya roki kwamitin NEC da ya kawo wa jam'iyyar APC ɗauki ta hanyar warware waɗannan basussuka da suka yi wa jam'iyyar katutu.
An tsaurara tsaro a sakatariyar APC
A wani rahoton, kun ji cewa manyan ƙusoshin APC sun hallara kuma an tsaurara matakan tsaro a sakatariyar APC da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan
Bayan kalaman El Rufai, Tinubu, Shettima, Ganduje sun kira taron kusoshin APC a Abuja
Shugabanni da jiga-jigan APC sun hallara a Abuja ne domin halartar taron kwamitin zartarwa na ƙasa watau NEC ranar 26 ga watan Fabrairu, 2025.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng