Tsohon Shugaban Ƙasa, Jonathan Ya Fallasa Yadda Ake Murɗe Zaɓe a Najeriya

Tsohon Shugaban Ƙasa, Jonathan Ya Fallasa Yadda Ake Murɗe Zaɓe a Najeriya

  • Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya ce har yanzu Najeriya ba ta iya shirya sahihi kuma ingantaccen zaɓe
  • Jonathan ya ce ya kamata a samu shugaban hukumar zaɓe watau INEC da kwamishinoni waɗanda za su yi murabus idan aka nemi su murde zaɓe
  • Tsohon shugaban ya kuma bayyana cewa banbancin yanki na kara maida Najeriya baya wajen samun nagartattun shugabanni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa Najeriya ba ta iya tantance adadin kuri’u na gaskiya da aka kaɗa a kowane irin zaɓe.

Jonathan ya ce hukumar zaɓe watau INEC ba ta iya ƙidaya sahihan ƙuri'u kaɗai a zabe saboda abin da ya kira "masu kada kuri’a na bogi."

Goodluck Jonathan.
Jonathan ya bayyana yadda ake shirya makarkashiya a zabuƙan Najeriya Hoto: Dr. Goodluck E. Jonathan
Asali: Getty Images

Jonathan ya bayyana hakan ne a wani taro da ƙungiyar Yianga Africa ta shirya kan yanayin zaɓe a Yammacin Afirka wanda aka gudanar a Abuja ranar Talata, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Tinubu ya fadi kudaden da ake ba gwamnonin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Goodluck Jonathan ya tona yadda ake murɗe zaɓe

A cewarsa, Najeriya ba za ta iya shirya ingantaccen zaɓe ba har sai shugabanni sun cire son rai, sun bar jami'an hukumar INEC sun yi aiki bisa gaskiya da adaci.

Ya ce ba za a iya yin sahihin zaɓe a Najeriya ba har sai an samu shugaban INEC da sauran jami'ansa da za su iya hakura su yi murabus idan aka matsa su murɗe zaɓe.

“A Najeriya, ba za ku taba samun adadin kuri’u na gaskiya ba, saboda mu na da masu kada kuri’a na bogi da yawa. Dole ne mu samu kwararru masu gaskiya a INEC," in ji Jonathan.

Tsohon shugaban kasar ya ce shugabanni masu son mulki da karfi suna matsa wa jami’an INEC lamba domin murde zabe a Najeriya.

Yadda za a gyara tsarin zaɓen Najeriya

Ya kara da cewa:

"Ya fi dacewa shugaban INEC da jami’ansa su yi murabus maimakon su yarda a tilasta musu aikata ba daidai ba."

Kara karanta wannan

Attahiru Jega ya gano matsalar dimokuradiyya a Afirika, ya fadi mafita

“Idan ka yarda da mukamin shugaban INEC ko kwamishina, ya kamata ka zama cikin shirin murabus matukar aka matsa maka lamba kan murde zabe. Idan ba mu da irin wadannan mutanen, to muna cikin matsala,” in ji shi.

Jonathan ya jaddada cewa har sai an samu shugabanci mai nagarta a INEC, tsarin zabe zai ci gaba da kasancewa da matsaloli.

Jonathan.
Jonathan ya jero matakan da ya kamata a ɗauka domin gyara tsarin zaɓen Najeriya Hoto: @YIANGA
Asali: Twitter

Jonathan ya ba da mafita

Ya kuma bukaci a gina tsari mai inganci da zai tabbatar da zabe na gaskiya da adalci, inda ba za a iya yin magudi ba.

“Idan dukkan jam’iyyun siyasa suna da karfi, kuma aka toshe hanyar murde zabe, mutanen da suka cancanta ne kaɗai za su kada kuri’a, sannan ne za a samu adadin kuri’u na gaskiya,” in ji shi.

Bugu da kari, tsohon shugaban kasar ya ce bambance-bambancen yanki na hana Najeriya samun shugabanni nagari.

Dr. Jonathan ya ce wannan matsala ta shiga kowane fanni na rayuwa har ma da addinai, yana mai cewa lokaci ya yi za a haɗa kai, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Jonathan ya tuna baya, ya fadi abin da ya so haddasa rikici a Najeriya

Shugaba Jonathan ya tuna zaɓen 2015

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana yadda zaɓen 2015 ya kusa tayar da zaune tsaye a Najeriya.

Jonathan ya ce na’urar tantance katin zaɓe ta ƙi karɓar shi da matarsa da mahaifiyarsa, sannan ta kusa haddasa rikici a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262