Tinubu zai Sauke Ganduje a Shugaban APC? Sakataren Jam'iyya Ya Magantu

Tinubu zai Sauke Ganduje a Shugaban APC? Sakataren Jam'iyya Ya Magantu

  • APC ta musanta rade-radin cewa Bola Tinubu zai tilastawa Abdullahi Ganduje yin murabus daga rike shugabancin jam’iyya na kasa
  • Sakataren jam’iyyar APC, Sanata Ajibola Basiru, ya ce taron NEC ba na zabe ba ne, kuma ba zai kawar da Ganduje daga shugabanci ba
  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya tabbatar da cewa ba zai halarci taron ba, kuma ya fadi dalilai kan hakan a wata hira da ya yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Yayin da aka fara shirye-shiryen babban taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC (NEC), shugabancin jam’iyyar ya yi magana kan makomar Abdullahi Ganduje.

Sakataren APC ya musanta rade-radin cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na shirin tilastawa Abdullahi Umar Ganduje yin murabus.

Kara karanta wannan

Bayan saukar farashin abinci, Tinubu ya yi magana kan tallafin man fetur

Ganduje
APC ta yi magana kan makomar shugabancin Ganduje. Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Asali: Facebook

Sanata Ajibola Basiru, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da jaridar The Punch, inda ya ce labarin tsige Ganduje kawai shaci-fadi ne da wasu ke yadawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Babu wani abu makamancin haka. Taron NEC na yau da kullum ne, ba taron zabe ba ne.
"Tun watan Satumba na bara ake kokarin gudanar da shi, amma yanzu an tabbatar da cewa za mu yi taron kwamitin jam’iyya a ranar Talata da kuma taron NEC a ranar Laraba.”

Me APC za ta tattauna a taron NEC?

Sanata Basiru ya bayyana cewa abin da za a tattauna a taron NEC ya kunshi nazarin shirin jam’iyyar na shekara ta 2025 da kuma bayani kan harkokin kudi kamar yadda doka ta tanada.

Ya ce za a tattauna batun sake yin rajistar mambobin jam’iyyar da za a fara nan ba da jimawa ba, tare da gabatar da rahoto kan cibiyar da APC ta kafa don bunkasa tunani da akidun siyasa.

Kara karanta wannan

Bayan kalaman El Rufai, Tinubu, Shettima, Ganduje sun kira taron kusoshin APC a Abuja

Sakataren ya ce wadannan batutuwan ne za a tattauna a taron jiga-jigan APC, inda za su duba makomar jam’iyyar a wani zaman da ake ganin zai kasance na musamman.

El-Rufa'i zai halarci taron jam'iyyar APC?

A gefe guda, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ba zai halarci taron NEC na APC ba.

Da yake magana a wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise TV, El-Rufai ya ce yana shirin tafiya kasar Masar a ranar taron.

A cewarsa,

“Ba zan samu damar halarta ba. Zan tafi birnin Cairo. Babu wani takaitaccen lokaci da aka ba ni game da taron.
Kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya bukaci a bai wa mambobi sanarwa a kalla kwanaki 14 ko 21 kafin irin wannan taro, amma ban samu sanarwar da wuri ba.”
El-Rufa'i
Tsohon gwaman Kaduna, Nasir El-Rufa'i. Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

Taron NEC na wannan karo shi ne irinsa na farko da Abdullahi Ganduje zai jagoranta tun bayan hawansa shugabancin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

'Ku tambaye shi, ya sani': El-Rufai ya fadi yadda Buhari ya tilasta masa neman gwamna

Jigon APC ya yi martani ga El-Rufa'i

A wani rahoton, kun ji cewa wani jigon APC a Kudu maso Kudu ya yi martani ga Nasiru El-Rufa'i kan maganar hadaka da Arewa.

'Dan siyasar ya ce a yanzu haka suna goyon bayan Bola Tinubu, sai dai El-Rufa'i ya hakura zuwa 2031 kafin ya fara maganar hadakar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng