El Rufa'i: APC Ta Hango Barazana a 2027, Ta Bukaci Tinubu Ya Dauki Mataki

El Rufa'i: APC Ta Hango Barazana a 2027, Ta Bukaci Tinubu Ya Dauki Mataki

  • Wata kungiya ta APC a Kudu Maso Gabas ta yi gargadi kan barazanar da ke tattare da siyasar Bola Tinubu a yankin
  • Kungiyar ta zargi Ministan Ayyuka, David Umahi, da dakatar da muhimman ayyukan tituna a Kudu maso Gabas
  • A karkashin haka, kungiyar ta bukaci shugaba Tinubu da ya binciki lamarin domin gujewa matsaloli a zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu - Wata kungiyar APC ta SARM ta yi gargadi kan barazanar da ke tattare da siyasar Bola Tinubu a yankin Kudu Maso Gabas.

Kungiyar ta zargi Ministan Ayyuka, David Umahi, da dakatar da ayyukan gina babbar hanyar Enugu-Onitsha, wanda hakan ke barazana ga makomar APC a yankin.

Tinubu
Kungiyar APC ta gargadi Tinubu a kan zaben 2027. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

The Guardian ta wallafa cewa kungiyar ta ce dakatar da titin na janyo matsaloli da cikas ga zirga-zirga, wanda hakan ka iya shafar yunkurin jam’iyyar APC wajen samun goyon baya a 2027.

Kara karanta wannan

An bankado umarnin Tinubu da zai illata Arewa, NARTO ta gargadi gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar SARM ta zargi Umahi

Shugaban kungiyar SARM, Osita Okechukwu, ya zargi Minista Umahi ya hana ci gaba da aikin titin Enugu-Onitsha mai tsawon kilomita 110, wanda ake ginawa karkashin shirin MTN RITCS.

A cewar Okechukwu, aikin titin yana tafiya cikin tsari kafin Umahi ya bayar da umarnin dakatar da shi, lamarin da ya haddasa tsaiko ga ci gaban yankin.

Ya kara da cewa rashin kammala aikin titin ya janyo matsaloli, ciki har da hadurran mota da gobarar tankar mai da ta yi sanadiyyar rasuwar mutane da dama.

Martanin Umahi da bukatar bincike

Da aka tambayi Ministan Ayyuka, David Umahi, kan wadannan zarge-zarge, sai ya mayar da martani a takaice yana mai cewa zargin ba shi da tushe.

Duk da haka, kungiyar SARM ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dauki mataki kan lamarin, tare da bincike don gano dalilin da ya sa aka dakatar da aikin titin.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya yi albashir ga Arewa kan matsalar ta'addanci, ya tabo alaka da Nijar

Okechukwu ya bayyana cewa dakatar da aikin titin zai iya kawo cikas ga kokarin jawo wa APC magoya baya a yankin Kudu Maso Gabas kafin zaben 2027.

Barazanar rage karfin APC a yankin

Okechukwu ya ce yana da mamakin yadda Minista Umahi ya ke barazanar soke kwangilar gina titin Enugu-Onitsha da MTN ta bayar kan kudi Naira biliyan 202.

Jaridar Blueprint ta wallafa cewa kungiyar ta bayyana cewa rashin kammala aikin titin zai kara rage goyon bayan da APC ke samu a yankin.

Lamarin na zuwa ne yayin da Nasir El-Rufa'i ya nemi yain hadaka da yankin domin abin da ya kira shirin ceto Najeriya.

Nasir
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufa'i Hoto: @Elrufai
Asali: Facebook

Bukatar Tinubu ya tsoma baki

SARM ta bukaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta tsoma baki don kare muradun APC a yankin Kudu Maso Gabas.

A cewar kungiyar, rashin kammala aikin titin da kuma rage wasu muhimman sassa na wasu tituna da fitilun hasken rana, zai kara dagula al’amura.

Kara karanta wannan

2027: El-Rufai ya fadi yankin da ya dace ya hada kai da Arewa domin ceto Najeriya

Kungiyar ta ce yana da muhimmanci a tabbatar da ci gaban yankin, tare da kawar da duk wani shakku da ka iya shafar APC a siyasar 2027.

Okechukwu ya ce:

"Ya Shugaban Kasa, wannan mataki yana da muhimmanci don ci gaban Ndigbo da nasarar gwamnatinka,"

Ganduje ya yabi Tinubu kan saukar farashi

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya ce gwamnatin Bola Tinubu tana tafiya a kan daidai.

Abdullahi Ganduje ya ce a yanzu haka farashi abinci ya sauka kuma farashin man fetur ma ya yi kasa sakamakon tsare tsaren Bola Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng