"Yana Raye ko Ya Mutu?": Watanni 3 ba a Ga Mataimakin Gwamna ba, an Fara Tada Jijiyoyin Wuya
- Rashin sanin wurin da mataimakin gwamnan jihar Taraba, Alhaji Aminu Alkali yake na ci gaba da jan hankalin ƴan adawa
- Jam'iyyar APC mai adawa a Taraba ta bukaci Gwamna Agbu Kefas ya fito ya yi wa al'umma bayanin halin da mataimakinsa ke ciki
- Wani lauya mai sharhi kan al'amuran da duka shafi kundin tsarin mulki ya ce haramun ne a doka gwamna da mataimkinsa su yi tafiya lokaci ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Taraba - Jam’iyyar APC reshen Taraba ta bukaci Gwamna Agbu Kefas ya gaggauta bayyana wa al’ummar jihar inda mataimakin gwamna, Alhaji Aminu Alkali, yake.
APC ta yi wannan kira ne a daidai lokacin da ake surutu kan lafiyar mataimakin gwamnan da kuma wurin da yake kasancewar an jima ba a ji ɗuriyarsa ba.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30

Asali: Twitter
APC ta bukaci bayani daga gwamna
Mai magana da yawun APC a jihar, Mista Aeron Atimas, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da jaridar Leadership a Jalingo ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Muna bukatar (Gwamna Agbu Kefas) ya faɗa mana inda mataimakin gwamnan Taraba yake," in ji shi.
APC ta yi kira ga gwamnan da ya bayyana gaskiya kan halin da mataimakinsa ke ciki, domin kuwa ’yan jihar na da hakkin sanin halin da shugabanninsu ke ciki.
"Mutane sun zaɓi mataimakin gwamna ne domin ya masu aiki, ba mallakin gwamna ba ne. Idan yana jinya, ya kamata majalisar dokoki ta kafa kwamitin likitoci domin tantance lafiyarsa," in ji Atimas.
Watanni 3 ba a ga mataimakin gwamna ba
Ya ƙara da cewa mataimakin gwamnan ya daina zuwa aiki na tsawon watanni uku, kuma al’ummar jihar Taraba na bukatar jin dalili.
Wani lauya mai sharhi kan kundin tsarin mulki, Barista P. D. Pius, ya bayyana cewa haramun ne a a doka gwamna da mataimakinsa a su bar jiha lokaci guda.
A cewarsa, Sashe na 176(1) na kundin tsarin mulki ya tabbatar da ofishin gwamna a matsayin babban jami’in zartaswa na jiha, yayin da sashe na 186 ya kafa ofishin mataimakin gwamna domin maye gurbin gwamna idan bai nan.
“Idan gwamna ya bar jiharsa na fiye da kwana 21, dole majalisar dokoki ta ayyana mataimakin gwamna a matsayin mukaddashi,” in ji lauyan.

Asali: Facebook
Lauya ya yi sharhi kan lamarin
Lauyan ya yi karin haske da cewa idan gwamna ya tafi hutu ko ya yi tafiya, dole mataimakinsa ya kasance yana aiki.
Pius ya tuna yadda Majalisar Dokokin Tarayya ta aiwatar da dokar bukatar gaggawa a lokacin rashin lafiyar marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua.
A cewarsa, hakan ya bai wa Goodluck Jonathan damar zama mukaddashin shugaban ƙasa.
"Idan Gwamna ya bar jiharsa, ba zai yiwu mataimakinsa ma ya bar ta ba," in ji shi.
Gwamna Kefas ya ɗauki zafi kan tsaro
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Taraba karkashin jagorancin Gwamna Agbu Kefas ta sha alwashin tube rawanin duk sarkin da ke da hannu a matsalar tsaro.
Gwamna Kefas ya bayyana haka ne yayin da yake nuna ɓacin ransa kan rikicin ƙabilancin da ya auku a ƙaramar hukumar Karim Lamido.
Asali: Legit.ng