'Yan Majalisa 27 Sun Tattara Kayansu Sun Fice daga Jam'iyyar APC? An Samu Bayanai

'Yan Majalisa 27 Sun Tattara Kayansu Sun Fice daga Jam'iyyar APC? An Samu Bayanai

  • Majalisar dokokin jihar Legas ta musanta rahoton da ake yaɗawa cewa ƴan Majalisa 27 sun fice daga APC zuwa jam'iyyar LP
  • Shugaban kwamitin yaɗa labarai na Majalisa ya ce babu mutum ɗaya daga cikin mambobin da ke tunanin sauya sheka zuwa wata jam'iyya
  • Wannan jita jita na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar dokokin ke fama da rikicin cikin gida tun bayan tsige tsohon kakaki, Mudashiru Obasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Mambobin Majalisar Dokokin Jihar Legas guda 27 sun karyata jita-jitar da ke cewa sun fice daga jam’iyyar APC mai mulki, sun koma LP.

Jita-jitar sauya shekar na zuwa ne yayin da rikicin siyasa ke kara kamari a majalisar, musamman dangane da yunkurin tsohon kakaki, Mudashiru Obasa, na dawowa kujerarsa.

Majalisar Legas.
Yan Majalisar dokokin jihar Legas 27 sun musanta sauya sheka daga APC zuwa LP Hoto: @Ishaofficial
Asali: Twitter

Obasa, wanda aka tsige daga mukaminsa a ranar 13 ga Janairu, 2025, ya garzaya kotu makon da ya gabata domin kalubalantar tsige shi, kamar yadda The Nation ta kawo.

Kara karanta wannan

Bayan tsige babban alkalin jiha, majalisa ta dakatar da mambobi 13 da suka janye

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya shigar da kara a babbar kotun Legas da ke Ikeja, yana ikirarin cewa ‘yan majalisar sun dauki matakin da ya saɓa doka, domin an tsige shi a lokacin da majalisa ke hutu.

Ƴan Majalisa 27 sun fice daga APC?

A wata sanarwa da mai magana da yawun majalisar, Hon. Ogundipe Stephen Olukayode, ya fitar, ya ce babu wani dan majalisa da ke shirin ficewa daga jam’iyyar APC.

Da yake martani kan raɗe-raɗin sauya shekar, kakakin majalisar ya ce:

“Majalisar dokokin jihar Legas ta musanta labarin da ke yawo cewa wasu mambobi 27 na shirin ficewa daga jam’iyyar APC zuwa LP, labarin ba gaskiya ba ne.
"Wannan rahoto karya ne kuma an kirkiro shi ne da nufin haddasa rudani a cikin majalisa da jefa waswasi tsakanin al’ummar jihar Legas.”

Majalisa ta bi doka wajen tsige Obasa

Sanarwar ta ci gaba da cewa tsige Mudashiru Obasa da maye gurbinsa da sabuwar kakaki, Rt. Hon. Mojisola Meranda, al’amura ne na cikin gida da aka aiwatar bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a fusata, sun ta aika kakkausan sako ga gwamnatin Tinubu

“Ba wani mamba a cikin majalisar da ke tunanin barin APC kuma muna nan daram domin ci gaba da aiwatar da kudirorin da suka dace da muradin al’ummar Legas.”

‘Yan majalisar sun yi kira ga shugabannin jam’iyya da magoya baya da su kwantar da hankalinsu, domin babu rikici da zai sa wani daga cikinsu ya sauya sheka.

A karshe, sun bukaci kafofin yada labarai da su rika bincike kafin su wallafa wani rahoto domin gujewa yada jita-jita da ka iya tayar da zaune tsaye a cikin al’umma.

Kakakin majalisar Legas ta yi murabus?

Kuna da labarin cewa sabuwa kakakin Majalisar dokokin jihar Legas, Hon Meranda ya karyata rahoton da ke cewa ta yi murabus daga muƙaminta.

Ta bayyana cewa tana nanan daram a kujerarta kuma ba ta tunanin murabus domin a yanzu ta maida hankali kan ayyukan da ke gabanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262