Cacar Baki Ta Balle Tsakanin APC, NNPP kan Yi wa Gwamnatin Abba Gida Gida Kishiya

Cacar Baki Ta Balle Tsakanin APC, NNPP kan Yi wa Gwamnatin Abba Gida Gida Kishiya

  • Jam’iyyar NNPP ta shiga takaddama da wata ƙungiyar APC, bayan sanarwar kafa gwamnati mai sa ido kan mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf a Kano
  • Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya, ya bayyana wannan ƙuduri a matsayin matakin haɗari ga dimokuraɗiyya
  • Ya ce bai dace tsananin adawa da rashin tasiri a jihar ya sa APC ta rufe idanunta wajen yin adawar da za ta zaba barazana ga kasar nan baki daya
  • Masanin siyasa, Salihi Yusuf Yakasai, ya bayyana cewa babu wani tsarin kafa gwamnatin sa ido a Najeriya, kuma yin hakan ya saba wa doka da oda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Jam’iyyar NNPP ta shiga takaddama da Patriotic Volunteers, wata ƙungiya a cikin jam’iyyar adawa ta APC a jihar Kano.

Kara karanta wannan

"Menene hujjar ku?" PDP ta karyata kitsa kai wa APC hari a Zamfara

Wannan ya biyo bayan sanarwar da ƙungiyar ta yi na niyyar kafa abin da ta kira “shadow government” don sa ido kan mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Gwamnati
Gwamnatin Kano ta yi tir da adawar APC Hoto: @OfficialAPCNg, @Kyusufabba
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya, ya bayyana cewa, ƙudurin ƙungiyar haɗari ne ga zaman lafiyar jihar da tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Abba ta yi martani ga APC

Kwamishinan ya ce dimokuraɗiyya ba ta ba kowa damar rasa hankalinsa ba, kawai don ya rasa tasiri a cikin tsarin siyasar jam’iyyarsa.

Kwamared Wayya ya ƙara da cewa ƴancin faɗar albarkacin baki ba ya ba mutum damar yin maganganun da ba su dace ba ko ɗaukar matakan da za su lalata tsarin mulki da ikon gwamnati da aka zaɓa.

Ya ce:

“Bari in tunatar da waɗannan mutanen APC a Kano cewa, a cikin tsarin dimokuraɗiyya kamar namu, kafa gwamnati a cikin wata gwamnati abu ne da bai halatta ba kuma ba ya cikin tsarin mulkinmu.

Kara karanta wannan

APC ta yi raddi ga Tambuwal, ta fadi dalilin raba garinsa da jam'iyyar

A Turai, musamman a Ingila, tsarin gwamnati a cikin wata gwamnatin na cikin tsarin majalisa ne, inda jam’iyyun adawa ke naɗa ministoci don sanya idanu kan ayyukan gwamnati mai ci.”

Menen matsayin gwamnatin sa ido a Najeriya?

Wani masanin siyasa a Kano, Salihi Yusuf Yakasai, ya bayyana wa majiyar Legit cewa babu tsarin samar da gwamnatin sa ido a tsarin shugabancin da Najeriya ke amfani da shi.

Ya ce:

“Saboda haka yin sa, haramtaccen abu ne kuma bai kamata ba. A hausance idan an ce ‘shadow government,’ ana nufin cewa wasu jami’ai na bogi ne da za su shiga cikin hukumomin gwamnati su na leƙen asiri.”

Ya ƙara da cewa wannan bidi’a ce a siyasar Najeriya, kuma hakan na iya jawo rikici da matsaloli a siyasar ƙasar nan.

APC na shirin yi wa gwamnatin Abba kishiya

A wani labarin, kun ji cewa Jam’iyyar APC ta bayyana shirin kafa gwamnati basaja a Kano domin sanya ido kan yadda da mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ke tafiya a jihar.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugaban ƙungiyar masu kishin APC a jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, yayin wani taro da ƙungiyar ta gudanar don sabunta shirye-shiryenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.