"Zan Fara Magana domin Al'umma," Kakakin APC Ya Gaji, Ya Yi Murabus Nan Take
- Sakataren yaɗa labaran APC na jihar Imo, Cajetan Duke ya yi murabus daga mukaminsa ranar Juma'a, 14 ga watan Fabrairu, 2025
- Duke, wanda ya ce ya jingine yaɗa ra'ayoyin APC, ya bayyana cewa lokaci ya yi da zai fara magana domin amfanin sauran al'umma
- Ana raɗe-raɗin wasu shugabannin APC a jihar Imo na shirin ajiye muƙamansu saboda matsin lamba da kuma nuna masu wariya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
jihar Imo - Mai magana da yawun jam’iyyar APC reshen jihar Imo, Cajetan Duke, ya yi murabus daga mukaminsa ba tare da wani bata lokaci ba.
Mista Duke ya bayyana cewa lokaci ya yi da zai yi magana domin amfanin al’umma gaba ɗaya maimakon fifita ra’ayoyin jam’iyyarsa ta APC.

Asali: Facebook
Cajetan Duke ya wallafa wasikar murabus dinsa a shafinsa na Facebook ranar Jumma’a, 14 ga Fabrairu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon kakakin APC ya bude sabon babi
Jigon ya ce:
"Yanzu za mu fara magana da yawun al'umma kuma don amfaninsu, na daina magana da yawun APC, mun buɗe sabon babi.
A cikin wasikar murabus dinsa wacce aka aika wa shugaban jam’iyyar APC na jihar, ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da iyalansa da abokan siyasa.
Dalilin kakakin jam'iyyar APC na yin murabus
Mista Duke ya ce ya yanke shawarar murabus daga mukamin don mayar da hankali kan maslaha da bukatun al’umma.
Wasikar murabus din ta ce:
"Bayan shawara da iyali da abokan siyasa, na yanke shawarar ajiye mukamina a matsayin sakataren yaɗa labarai na APC a jihar Imo, daga yau, 14 ga Fabrairu, 2025."
"Ina godiya ga damar da aka bani na yin hidima wa jam’iyya da kuma alaƙa mai kyau da na ƙulla da shugabanni da ‘yan jam’iyya. Ina mai godiya da gogewa da darussan da na samu."
An fara nunawa kusoshin APC wariya
Wata majiya ta bayyana cewa da yiwuwar a samu karin murabus daga wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a makonnin nan masu zuwa, kodayake ba a bayyana dalilan hakan ba.
Jim kaɗan bayan haka, Barista Kissinger Ikeokwu, tsohon lauyan PDP a Imo, ya ce Duke da wasu abokan aikinsa sun fuskanci matsin lamba da wariya a APC, wanda ka iya zama dalilin fara ajiye mukamansu.
APC ba ta bukatar Kwankwaso a Kano
Kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi ikirarin cewa jagoran NNPP na ƙasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya fara kamun ƙafa da nufin dawowa cikinta.
Mai magana da yawun APC a Kano, Ahmed S. Aruwan ya ce ba su bukatar tsohon gwamnan, ya yi zamansa a NNPP domin za su lashe zabe ko babu shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng