Jam'iyyar PDP Ta Dare Gida 2, Sabon Rikici Ya Mamaye Manyan 'Yan Adawar Tinubu

Jam'iyyar PDP Ta Dare Gida 2, Sabon Rikici Ya Mamaye Manyan 'Yan Adawar Tinubu

  • Rikicin cikin gida ya barke a jam’iyyar PDP reshen Kudu maso Kudu sakamakon wani taro da Cif Dan Orbih ya kira a Benin, jihar Edo
  • Sakataren jam'iyyar na shiyyar, Cif Felix Omemu, ya bayyana taron a matsayin haramtacce, inda ya nemi 'ya'yan jam'iyyar su ki halarta
  • Ya kuma yi kira ga shugabannin PDP da su dakatar da taron, yana zargin cewa an shirya shi ne domin cimma wata manufa ta daban

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Jam’iyyar PDP a Kudu maso Kudu ta tsinci kanta cikin rikici bayan wani taro da aka shirya a garin Benin, jihar Edo, a ranar 15 ga Fabrairu.

Taron ya gudana ne karkashin mataimakin shugaban PDP na yankin Kudu maso Kudu, Cif Dan Orbih, wanda hakan ya haifar da ce-ce-ku-ce.

Kara karanta wannan

Rikicin APC ya fito fili, shugabanni na harbin juna da bakaken maganganu

Rikicin cikin gida ya kunno kai a cikin jam'iyyar PDP reshen Kudu maso Kudu
Shirya taro ya jawo rigima ta barke a jam'iyyar PDP reshen Kudu maso Kudu. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Sabani ya barke a tsakanin jagororin PDP

Sakataren PDP na shiyyar, Cif Felix Omemu, ya soki wannan taro, yana mai bayyana shi a matsayin haramtacce, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin ya kara daukar zafi da Cif Felix Omemu ya gargadi 'ya'yan jam’iyyar da kada su kuskura su halarci taron da Cif Dan Orbih ya kira.

Omemu ya ce taron ya saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar, wanda ke tanadar cewa dole ne a samu amincewar kwamitin gudanarwa na shiyyar kafin kiran taro.

"Taron ya sabawa kundin mulkin PDP" - Sakatare

Cif Felix ya kara da cewa mataimakin shugaban bai samu amincewar 'yan kwamitin ba, wanda hakan ya sa taron ya zama haramtacce.

Sakataren PDP ya ce:

“A cewar sashe na 26, (2c) na tsarin mulkin PDP da aka gyara a 2017, taro ba zai gudana ba tare da amincewa kwamitin aiki na shiyyar ba.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin tarayya ta nemi ba ni rashawar N5bn," Ɗan takarar shugaban ƙasa

“Bayan haka, a matsayina na sakataren jam'iyyar na wannan shiyya, ba ni da masaniya kan wannan taro, kuma ba zan goyi bayan wannan haramtaccen taro ba."

Sakataren PDP ya nemi a dakatar da taron

Ya yi kira ga shugabannin PDP na yankin Kudu maso Kudu da su kaurace wa taron, yana zargin cewa an shirya taron ne domin cimma wani manufa mara amfani ga jam’iyyar.

Cif Felix ya ce:

“Ina rokon shugabannin PDP a yankin da kada su halarci wannan taro mai cike da zarge-zarge kuma mai yiwuwa ba zai amfani jam’iyya ba.
“Na kuma yi kira ga gwamnoni, tsoffin gwamnoni, ’yan majalisar dokoki, da shugabannin PDP daga yankin da su dakatar da Cif Orbih daga gudanar da taron."

Ya ce yana fatan shugabannin jam’iyyar za su dauki mataki domin kauce wa duk wani mummunan sakamako da wannan taro zai iya haifarwa.

Kara karanta wannan

APC na yi wa jam'iyyar adawa dauki dai-dai, dan majalisar PDP ya sauya sheka

PDP ta dare, an samu sabon shugaba

A wani labarin, mun ruwaito cewa, lamura sun dagule a PDP reshen Katsina bayan rikici ya ɓarke tsakanin Sanata Yakubu Lado da Mustapha Inuwa.

Tsagin Lado ya rantsar da shugabannin jam’iyya sababbi, yayin da Mustapha Inuwa ya ce tawagarsa za ta garzaya kotu don neman haƙƙinta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.