Ganduje Ya ba 'Yan Arewa Shawara kan Yin Takara da Tinubu a Zaben 2027
- Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ya ba Arewa masu son yin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 shawara
- Abdullahi Umar Ganduje ya buƙaci ƴan Arewa da su haƙura da burinsu na yin takara da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027
- Shugaban na APC ya jaddada cewa da yardar Allah sai shugaba Tinubu ya yi shekara takwas yana kan madafun iko a Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan ƴan Arewa da ke burin yin takara da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Abdullahi Ganduje ya shawarci ƴan Arewa masu wannan niyyar da su haƙura da batun yin takarar shugaban ƙasa da Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta rahoto cewa Ganduje ya jaddada cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kammala wa’adin mulkinsa na shekara takwas.

Kara karanta wannan
'Komai ya wuce': El Rufai ya fadi manyan dalilai 3 na tallata Tinubu a zaben 2023
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace shawara Ganduje ya ba ƴan Arewa?
Ganduje ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga tsohon gwamnan Kaduna, Mal. Nasir El-Rufai, wanda ya wallafa a shafinsa na X.
Sakon ya nuna cewa mutanen Arewa za su iya yi wa gwamnatin Bola Tinubu irin abin da aka yi wa Goodluck Jonathan a 2015.
Abdullahi Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin da yake karɓar baƙuncin shugabanni da mambobin (PBAT Media Centre) da ƙungiyar matasa masoya Tinubu a Arewa (TNYF) a hedkwatar APC da ke Abuja.
Shugaban na APC ya ce duk wanda ke tunanin mulki zai koma Arewa a 2027 ya farka daga barci, domin hakan ba zai yi wu ba.
Ganduje ya jaddada cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da bin tsarin yin karɓa-karɓa tsakanin Kudu da Arewa.
Ganduje ya ce Tinubu zai ya yi takwas
"Lokacin da ɗan Arewa ya yi mulki na shekara takwas, mun nace cewa dole shugaban ƙasa na gaba a jam’iyyarmu ya fito daga yankin Kudu."

Kara karanta wannan
"Najeriya ta yi Rashi," Tinubu ya kaɗu da Allah ya yi wa fitaccen malamin Musulunci rasuwa
"Cikin ikon Allah, mun yi aiki tuƙuru tare da haɗin kan ƴan Najeriya, kuma shugaban ƙasa daga yankin Kudu ya hau mulki."
"Shugabanmu zai kammala wa’adin mulkinsa na farko, kuma da yardar Allah zai sake zarcewa a 2027. Daga nan ne mulki zai koma Arewa.”
- Abdullahi Umar Ganduje
Ganduje ya faɗi shirin APC kan zaɓen Anambra
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce lokaci ya yi da jam'iyyar za ta karɓe mulkin Anambra.
Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ya kamata APC ta karɓe mulkin jihar Anambra daga hannun Gwamna Chukwuma Soludo da jam'iyyar APGA.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng