"Baki Ke Yanka Wuya": Atiku Abubakar Ya Jawo Wa Kansa Abin Magana, An ba Shi Mafita

"Baki Ke Yanka Wuya": Atiku Abubakar Ya Jawo Wa Kansa Abin Magana, An ba Shi Mafita

  • Shugaban IPAC, Yusuf Dantalle ya ce Atiku Abubakar ya yi zargin da ba shi da tushe cewa shugabannin jam’iyyun adawa sun karɓi Naira miliyan 50 daga APC
  • Ya bayyana cewa a matsayinsa na shugaban IPAC ba shi da masaniya kan wani shugaba da ya karɓi irin wannan kuɗi
  • Yusuf Dantalle ya ce idan Atiku ba zai iya faɗin sunayen shugabannin da suka karɓi kuɗin ba, to ya nemi gafara don guje wa tada hargitsi a siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban IPAC, mai ba jam'iyyun adawa shawari, Yusuf Dantalle, ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya nemi afuwa.

Shugaban IPAC ya buƙaci Atiku ya fito ya ba da haƙuri kan ikirarinsa na cewa shugabannin jam’iyyun adawa suna karɓar kuɗi daga jam’iyya mai mulki watau APC.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun fara taɓa manya, an yi garkuwa da shugaban hukumar zaɓe ta jiha

Atiku Abubakar.
Shugaban IPAC ya buƙaci Atiku Abubakar ya ba shugabannin jam'iyyu haƙuri Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Yusuf Ɗantalle ya buƙaci hakan ne a wata hira da aka yi da shi a cikin shirin siyasa a yau na Channels tv ranar Juma'a, 31 ga watan Janairu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalaman Atiku da suka tayar da ƙura

Atiku ya yi ikirarin cewa Gwamnatin Tarayya tana ba wasu shugabannin jam’iyyun adawa Naira miliyan 50 domin haddasa rikici a cikinsu.

Da yake martani kan wannan zargin da Atiku ya yi, shugaban IPAC, Yusuf Dantalle ya ce ba zai dauki wannan zargi da wasa ba.

Shugaban IPAC ya ƙaryata Atiku

"Mai yiwuwa kai (Atiku) ka samu bayanai, amma hakan ba ya nufin ka fito ka ce an bai wa dukkan shugabannin jam’iyyun adawa Naira miliyan 50 ba.
"Ni shugaba ne na jam’iyyar APM, kuma ina jagorantar dukkan jam’iyyun siyasa a Najeriya. Ba ni da masaniya kan wani shugaba da ya karɓi irin wannan kuɗi,” in ji shi.

An buƙaci Atiku ya fito ya bada haƙuri

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan Majalisa ya danƙara wa Atiku baƙaken kalamai bayan abin da ya faru a taron BoT

Shugaban IPAC ya ce Atiku yana haifar da matsala a siyasar kasar nan tare da haddasa shakku da rashin fahimta tsakanin ‘yan adawa.

“Abin da nake fatan Atiku zai yi, cikin mutuntawa shi ne ya nemi gafarar shugabannin jam’iyyun adawa ta yadda yadda ya yi wannan zargi, ko kuma ya bayyana sunayen wadanda suka karɓi kuɗin."

Ya kuma bayyana cewa ya tattauna da shugabannin jam’iyyun siyasa daban-daban kuma sun nuna bacin ransu kan furucin Atiku, rahoton Vanguard.

Atiku ya hango matsalar demokuraɗiyya

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa ɓangaren shari'a ne babbar matsalar da ta addabi demokuraɗiyya.

Wazirin Adamama ya ce duk da gyare-gyaren da ake cewa an yi a fannin shari'a, har yanzu babu canji da aka samu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel