Abin da Shugaban BoT Ya Faɗa a Wurin Taron PDP bayan an Mari Babban Jigo a Abuja
- Shugaban BoT na PDP ta ƙasa, Sanata Adolphus Wabara ya ce ya zama dole a shirya taron kwamitin zartarwa watau NEC nan kusa
- Wabara ya bayyana haka ne a taron BoT karo na 76 wanda rigima ta kaure kan rikicin kujerar sakataren PDP na ƙasa a Abuja ranar Laraba
- Ya kuma soki gwamnatin APC yana mai cewa har yanzun ƴan Najeriya na kallon PDP a matsayin jam'iyyar da za ta iya ceton ƙasarsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban Majalisar Amintattu (BoT) na jam’iyyar PDP, Sanata Adolphus Wabara, ya jaddada cewa dole ne a gudanar da taron kwamitin zartarwa (NEC) da aka shirya yi a watan Fabrairu.
Sanata Wabara ya ce duk da rikicin shugabanci da ke ci gaba da addabar PDP, ya zama dole a shirya taron NEC nan kusa don warware wasu matsalolin.
![Taron BoT. Taron BoT.](https://cdn.legit.ng/images/1120/e7529e8b26ef4f4b.jpeg?v=1)
Asali: Twitter
Wabara ya yi wannan bayani ne a taron BoT karo na 79 da aka yi a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja a ranar Laraba, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda rigima ta ɓarke a taron BoT
Taron BoT na wannan karon ya zo da tashin-tashina, inda masu rigima kan kujerar sakatare, Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye suka yi arangama.
Rahoto ya nuna cewa faɗa ya kaure a wurin taron har sai ta kai ga marin Ude-Okoye tare da fitar da shi daga ɗakin taron da ƙarfin tsiya.
Rikicin ya yi ƙamari a jiya Laraba har dai da jami'an tsaro suka shiga tsakani, sannan komai ya lafa a hedkwatar PDP ta ƙasa.
Abin da shugaban BoT ya faɗa a taron
Da yake jawabi a wurin taron, shugaban BoT ya bukaci ƴan PDP a kowane mataki su haɗa kansu kuma ya ja hankalinsu da su fifita ci gaban jam’iyya fiye da bukatun kansu.
"Wannan taro ya zo ne a daidai lokacin da hadin kai, manufa, da ƙimar jam’iyyarmu ke fuskantar kalubale. Abin takaici ne har yanzu ba a warware rikicin shugabanci a kwamitin gudanarwa (NWC) ba.
"Rashin shawo kan wadannan matsaloli yana rage wa jam’iyyarmu mutunci," in ji Wabara.
Ya kamata PDP ta shirya taron NEC
Ya kara da cewa yana da matukar muhimmanci a gudanar da taron NEC kamar yadda aka tsara a wata mai kamawa.
"NEC ita ce mai alhakin yanke shawara a jam’iyyarmu, dole ne a gudanar da taron ba tare da bata lokaci ba domin mu tabbatar da an rungumi hadin kai, da’a, da manufofin da suka hada mu wuri guda."
Adolphus Wabara ya kuma caccaki jam’iyyar APC, yana mai cewa PDP ce kadai za ta iya ceto Najeriya, kamar yadda Punch ta ruwaito.
"Kasar mu tana wahala a karkashin mulkin APC. ‘Yan Najeriya na kallonmu a matsayin haske da fatansu na gari, dole ne mu cika wannan buri," in ji shi.
Damagum ya zargi wasu shugabanni a taron BoT
A wani labarin kun ji cewa muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa ya zargi wasu shugabanni da hannu a rura wutar rikicin da ke faruwa a NWC.
Umar Damagum ya ce lokaci ya yi da za a haɗa kai wuri guda domin farfaɗo da jam'iyyar PDP wacce ƴan Naheriya ke da sa rai a kanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng