Ganduje Ya Gamu da Gagarumar Matsala, Ƴan Tawagar Tsohon Gwamna Sun Fice daga APC

Ganduje Ya Gamu da Gagarumar Matsala, Ƴan Tawagar Tsohon Gwamna Sun Fice daga APC

  • Kungiyar Omoluabi ta tsohon gwamnan jihar Osun ta sanar da ficewarta daga jam'iyyar APC gabanin zaben gwamnan jihar na 2026
  • Sakataren yada labaran kungiyar ya bayyana cewa matsalolin cikin gida da rashin shugabanci na gari sun rage karfin APC a Osun
  • Tsohon gwamnan, Rauf Aregbesola ya yabawa mambobin kungiyar bisa jajircewarsu, ya na mai bayyana fa'idar ficewarsu daga APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Osun - Kungiyar Omoluabi, wata kungiyar siyasa karkashin tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, ta sanar da ficewarta daga jam'iyyar APC.

A cikin wata sanarwa daga sakataren yada labaran kungiyar da ya fitar a Osogbo a ranar Lahadi, kungiyar ta bayyana dalilin barin APC mai adawa.

Rauf Aregbesola ya yi magana da kungiyarsa ta fice daga jam'iyyar APC
Tsohon gwamnan Osun ya jaddada ficewar kungiyarsa daga jam'iyyar APC. Hoto: @raufaregbesola
Asali: Facebook

Kungiyar tsohon gwamna ta fice daga APC

Sakataren yada labaran, Oluwaseun Abosede ya shaida cewa kungiyar ta fice daga APC bayan amincewar masu ruwa da tsaki daga gundumomi 332, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan El Rufa'i ya kwance mata zani a kasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta cimma matsayar jefar da tafiyar siyasar jam'iyya mai mulki a taronta na wata wata da ya gudana a garin Ilesa.

Sanarwar ta bayyana cewa dalilan da suka saka kungiyar ficewa daga APC sun hada da rashin adalci da dakatar da 'yan kungiyar daga jam'iyyar ba tare da wani dalili ba.

Kungiyar ta bayyana dalilin ficewa daga APC

Kungiyar ta tsohon gwamnan ta ce shugabannin APC sun mayar da 'ya'yanta saniyar ware a dukkanin ayyukan da suka shafi jam'iyyar

Sakataren yada labaran kungiyar ya ce sun gaji da yadda jam'iyyar APC ke magance matsalolinta na cikin gida wadanda suka ja ta sha kaye a zaben jihar da ya gabata.

A cewar kungiyar, rashin iya shugabanci ya taimaka gaya wajen rage kimar jam'iyyar da karfinta a jihar Osun.

"Shugabannin kungiyar suka kada kuri'a, inda suka amince da sauya sheka zuwa wata jam'iyyar gabanin zaben gwamnan jihar na 2026 mai gabatowa."

Kara karanta wannan

APC ta yi kaca kaca da Atiku Abubakar, ta fadi wanda ke haddasa rikici a PDP

- A cewar sanarwar

Tsohon gwamnan ya jaddada ficewa daga APC

Da ya ke jawabi a wajen taron, Aregbesola, wanda shi ne tsohon ministan harkokin cikin gida, ya yawaba 'yan kungiyar bisa kokarinsu na riko da gaskiya da neman shugabanci na gari.

Channels ta rahoto tsohon gwamnan ya nemi 'yan kungiyar su zage damtse yayin da suka shirya daukar Omoluabi zuwa wani mataki mai girma a nan gaba.

Da yake tsokaci kan hukuncin kungiyar na ficewa daga APC, Aregbesola ya ce wannan zai zama sabon babi na samar da shugabanci mai kyau a jihar Osun.

"Dole Aregbesola ya nemi gafarar Tinubu" - Adesiyan

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon ministan harkokin yan sanda, Jelili Adesiyan, ya ce ya zama wajibi ga Rauf Aregbesola ya nemi gafarar shugaba Bola Tinubu.

Jelili Adesiyan ya ce yanayin yadda tsohon gwamnan na Osun ke gudanar da harkokinsa a APC ya yi kamar ba dan jam'iyyar ba, don haka ya nemi afuwar Tinubu don ya gyara furarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.