Kungiyoyi Sun Fadi Abin da zai Sa Tinubu Samun Karbuwa wajen Talaka a 2027

Kungiyoyi Sun Fadi Abin da zai Sa Tinubu Samun Karbuwa wajen Talaka a 2027

  • Tarin kungiyoyin matasa fiye da 20 a Neja Delta sun bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai samu abokin hamayya ba a zaben 2027
  • Kungiyoyin sun yaba wa salon jagorancin Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) karkashin Dr Samuel Ogbuku
  • Haka zalika matasan sun bayyana cewa hukumar NDDC tana aiwatar da ayyukan ci gaba da ke shafar rayuwar al’umma kai tsaye a yankin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Kungiyoyin matasa fiye da 20 daga yankin Neja Delta sun bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai samu abokin hamayya ba a zaben 2027.

Matasan sun fadi haka ne duba da gagarumin cigaban da Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) take samarwa karkashin jagorancin Dr Samuel Ogbuku.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Shugaba Tinubu
Matasan Neja sun goyi bayan Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

The Nation ta wallafa cewa kungiyoyin sun gudanar da taro a Fatakwal, jihar Ribas, inda suka yi nazari kan nasarorin da NDDC ta samu karkashin shugabancinta na yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata sanarwa da suka fitar bayan taron, matasan sun bayyana cewa ayyukan hukumar sun sa al’umma na jin dadin tsarin gwamnati da ke kula da bukatun su kai tsaye.

Gudunmawar Hukumar NDDC a Neja Delta

Kungiyoyin matasan sun ce sun ziyarci yawancin ayyukan da hukumar ta gudanar, ciki har da sababbin ayyuka da na baya da aka karasa, kuma sun yaba da ingancin ayyukan.

A cewar sanarwar da suka fitar, Dr Ogbuku da tawagarsa sun gudanar da ayyuka masu tasiri ga rayuwar mutane, wadanda suka shafi ci gaban yankin baki daya.

Shugabannin kungiyoyin, ciki har da Jesse Ese, Pastor Jude Teidor Olayinka, da Tonbra Kingdom Yeri, sun gode wa shugaba Tinubu bisa nadin kwararru a hukumar.

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Tasirin shirye-shirye da tsare-tsaren NDDC

Sanarwar ta bayyana cewa hukumar ta samu nasarar kafa tsare-tsare da suka shafi ilimi, lafiya, tattalin arziki, da sauran sassan rayuwa.

Matasan sun ce ana tabbatar da gaskiya da adalci a cikin shirin tallafin karatu na kasa da kasa da sauran shirye-shiryen hukumar.

Kungiyoyin sun yaba da yadda NDDC ke kula da bukatun jama’a ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba, suna mai cewa hakan ya dauki hankalin al’umma da jawo kaunar su ga Tinubu.

Sun bayyana cewa dangantakar hukumar da gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki a yankin ta kasance mai kyau, wanda hakan ke tabbatar da zaman lafiya da ci gaba.

Neja Delta za su goyi bayan Tinubu?

Kungiyoyin matasan sun ce gwamnatin Tinubu na samun gagarumin goyon baya daga yankin saboda tasirin ayyukan NDDC, wadanda ke shafar rayuwar jama’a kai tsaye.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 30 sun shiga har cikin daki sun sace mata da miji a Abuja

A cewarsu, tsarin da hukumar ke amfani da shi na sauraron ra’ayoyin jama’a da aiwatar da ayyuka bisa bukatun su ne ya kara wa gwamnatin Tinubu daraja a idon mutane.

Matasan sun kara da cewa tsarin tallafawa matasa da horar da su ya samu karbuwa sosai, duk da yawan mutane da ke neman shiga shirin.

Sun ce irin jagorancin ne ke nuna tasirin gwamnati ga rayuwar al’umma, wanda ke kara wa shugaba Tinubu goyon bayan da zai sa ya samu nasara ba tare da hamayya mai karfi ba a 2027.

Tinubu zai raba tallafin N4bn

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince ta raba tallafin kudi har Naira biliyan 4 ga 'yan kasa.

Dadin dadawa, shugaba Bola Tinubu ya amince da raba bashin Naira biliyan 2 ga manoma a fadin Najeriya domin yaki da yunwa a fadin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng