An Fara Tono 'Sirrin' Dan Tinubu bayan Fara Maganar Takararsa a 2027

An Fara Tono 'Sirrin' Dan Tinubu bayan Fara Maganar Takararsa a 2027

  • Wata kungiyar matasan jihar Legas ta yi watsi da kiran Ministan Matasa, Ayodele Olawande, na cewa Seyi Tinubu ya dace ya zama gwamna a 2027
  • Kungiyar ta yi zargin cewa Seyi Tinubu ba ɗan jihar Legas ba ne, kuma akwai isassun matasa da dattawan jihar da suka cancanci wannan matsayin
  • Kungiyar ta yi alkawarin nuna adawa da duk wani yunkuri na kakaba Seyi Tinubu kan kujerar gwamnan jihar Legas a zaben shekarar 2027

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Wata kungiya ta 'yan asalin jihar Legas ta yi watsi da kiran Ministan Matasa, Ayodele Olawande, na cewa Seyi Tinubu ya dace ya zama gwamnan Legas a 2027.

Kungiyar De Renaissance Patriots Foundation ta bayyana ra’ayin ne a cikin wata sanarwa da ta fitar, tana mai cewa kiran ministan ba ya wakiltar ra’ayin al’ummar jihar Legas.

Kara karanta wannan

Shugaba a APC ya yi zazzafan martani ga El Rufa'i kan hadaka da 'yan adawa

Seyi Tinubu
An fara sukar takarar Seyi Tinubu a 2027. Hoto: Aso Villa
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a sanarwar, kungiyar ta ce ta dauki furucin ministan matasan a matsayin zance maras tushe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Seyi Tinubu ba dan Legas ba ne inji matasa

Kungiyar ta yi ikirarin cewa Seyi Tinubu ba ya daga cikin 'yan asalin jihar Legas, tana mai cewa babu wata hujja da ke nuna dangantakarsa da kowanne yanki na jihar.

"Seyi Tinubu ba zai iya danganta kansa da wani yanki na jihar Legas ba, ko dai Epe, Badagry, Lagos Division, Ikeja, ko Ikorodu,"

- Kungiyar matasan Legas

Sun kara da cewa duk wata jiha da ke ganin Seyi ya dace da shugabancinta tana iya karbar shi, amma a matsayin matasan Legas, sun yi alkawarin kin amincewa da takararsa.

Zargin cefanar da jihar Legas

Kungiyar ta kuma zargi wasu dattawan jihar da neman amfani da matsayinsu domin sayar da makomar jihar ga masu mulki.

Matasan sun ce;

Kara karanta wannan

Tinubu ya bugi karji kan darajar Afrika a Qatar, ya fadi sirrin cigaban nahiyar

"Mun san wasu dattawa sun riga sun sayar da makomar jihar ga gwamnati mai ci, kuma suna shirin yin hakan nan gaba."
"Amma, mu na tabbatar musu cewa ba za mu yarda da wannan yunkuri ba,"

Sun kara da cewa matasan jihar Legas a yau sun fi karfi da himma fiye da na baya, kuma ba za su bari a yi amfani da su wajen kakaba masu dan takara ba tare da yardarsu ba.

Kungiya ta gargaɗi ga Seyi Tinubu

Kungiyar ta yi kira ga Seyi Tinubu da ya guji fadawa tarkon mutanen da ke kokarin kakaba masa takarar gwamna a jihar Legas.

Matasan sun ce;

"Legas ba kamar yadda ta kasance a baya ba ce. Muna da matasa da dattawan da za su iya jagoranci.
"Idan Seyi Tinubu ya dace ya yi takara, to ya gwada daga jihar Osun ko Oyo, inda mahaifiyarsa ta fito,"

Kara karanta wannan

Ndume: Matasan Arewa sun gana da Sanatan APC don dakile kudirin haraji a majalisa

Sun bayyana cewa jihar Legas tana da ɗimbin maza da mata da suka dace da kujerar gwamna, kuma ba za su lamunci tsarin mayar da siyasa tsarin sarauta ba a jihar.

Dalilin tsige kakakin majalisar Legas

A wani rahoton, kun ji cewa wani jigo a jami'iyyar APC ya bayyana wasu dalilai da suka sanya tsige kakakin majalisar jihar Legas.

An ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu ya yi kokarin sasanta rikicin da ya kunno a majalisar amma aka samu matsala daga bangaren kakakin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng