Rawar da Tinubu Ya Taka a Dambarwar Tsige Kakakin Majalisar Legas

Rawar da Tinubu Ya Taka a Dambarwar Tsige Kakakin Majalisar Legas

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi kokarin shawo kan rikicin majalisar dokokin jihar Legas kafin tsige tsohon Kakakin Majalisar, Mudashiru Obasa
  • Ana hasashen cewa Mudashiru Obasa ya rasa kujerarsa ne sakamakon zargin almundahana da rashin biyayya ga jagororin jam’iyyar APC
  • Ana zargin cewa maganganu masu cike da girman kai da ya yi a lokacin gabatar da kasafin kudin 2025 na jihar Legas na cikin dalilan tsige shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi yunkurin warware rikicin shugabancin majalisar dokokin jihar Legas a lokacin hutu na Kirsimeti.

Ana zargin cewa yunkurin ya ci tura sakamakon rashin biyayya daga bangaren Mudashiru Obasa.

Obasa
Yadda Tinubu ya yi kokarin sulhunta rikicin majalisar Legas. Hoto: Bayo Onanuga|Lagos State Government
Asali: Twitter

Jigon jam’iyyar APC, Fouad Oki ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da tashar Channels TV, inda ya ce shugaba Tinubu ya kira taro domin magance matsalar.

Kara karanta wannan

Shugaba a APC ya yi zazzafan martani ga El Rufa'i kan hadaka da 'yan adawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Litinin, ’yan majalisar suka tsige Obasa daga kujerar Kakakin Majalisar tare da zarginsa da cin hanci da rashin da’a, inda suka nada tsohuwar mataimakiyarsa, Mojisola Meranda.

Yunkurin Tinubu na sasanta rikicin majalisar Legas

Fouad Oki ya bayyana cewa tun kafin shugaba Tinubu ya dawo gida hutun Kirsimeti rikicin ya dade yana gudana.

A cewarsa, majalisar dattawan jam’iyyar APC (GAC) ce ta jawo hankalin Tinubu kan rikicin, ta bukaci ya taka rawa wajen kawo maslaha.

“Shugaban kasa ya yi kokarin shawo kan matsalar ta hanyar ganawa da shugabannin jam’iyya da ’yan majalisar,
"Amma rashin sassaucin Obasa ne ya sanya shirin bai samu nasara ba,”

- Fouad Oki

Ya kara da cewa matakin tsige Obasa ya biyo bayan rashin biyayyarsa ga shawarwarin dattawan jam’iyyar APC.

Dalilan tsige Obasa a jagorancin majalisa

Masu lura da siyasar jihar Legas sun bayyana cewa maganganun da Obasa ya yi lokacin gabatar da kasafin kudin 2025 sun taka muhimmiyar rawa wajen tsige shi.

Kara karanta wannan

'Yan Majalisa sun tsige kakakin Majalisar dokoki, sun zaɓi mace ta maye gurbinsa

Lokacin da gwamna Babajide Sanwo-Olu ya gabatar da kasafin 2025 a Nuwamban 2024, Obasa ya karkata daga batun kasafin kudin zuwa magana kan aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna.

Vanguard ta wallafa cewa a cikin jawabinsa, Obasa ya ce bai taba daukar batun takarar gwamna da muhimmanci ba, amma hakan ba yana nufin bai cancanci rike mukamin ba ne.

“Ban dauki batun takarar gwamna da muhimmanci ba, amma hakan ba yana nufin ba ni da gogewa ko cancantar yin hakan ba ne.
"Na kuma bayyana cewa na fi wadanda suka rike wannan kujera gogewa,”

- Mudashiru Obasa

Wasu sun fassara jawabin a matsayin girman kai da ya sanya wasu manyan jam’iyyar APC a Legas jin cewa Obasa ya saba wa tsarin jam’iyya.

Martanin masana kan tsige Obasa

Masu fashin bakin siyasa sun yi nuni da cewa rashin sassaucin Obasa wajen bin umarnin dattawan jam’iyya da kuma rashin nuna biyayya ga shugabanci ya jawo masa tsigewar.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun mamaye hedikwatar PDP bayan rikicin jam'iyya ya yi kamari

Fouad Oki ya kara da cewa;

“Matakin tsige Obasa ba abu ne da aka dauka da wasa ba. Yana da alaka da yadda ya kasa samun jituwa da jagororin jam’iyya.”

Har ila yau, an bayyana sabuwar Kakakin Majalisar, Mojisola Meranda a matsayin wadda ke da kwarewa kuma za ta iya tabbatar da hadin kan majalisar.

Matasa sun taru a majalisar Legas

A wani rahoton, kun ji cewa a ranar Litinin aka tsige kakakin majalisar Legas yayin da yake halin tafiya zuwa kasar waje.

Legit ta wallafa cewa bayan tsige kakakin, an hango wasu matasa a farfajiyar majalisar dauke da wasu abubuwa da suka nuna alamar tsafe tsafe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng