Yadda Zargin Peter Obi Ya Jefa Rayuwarmu a cikin Barazana," Kakakin APC

Yadda Zargin Peter Obi Ya Jefa Rayuwarmu a cikin Barazana," Kakakin APC

  • Kakakin APC, Felix Morka, ya ce yana fuskantar barazanar kisa fiye da 400, ciki har da 200 da aka bayyana yadda za a kashe shi
  • Morka ya ƙaryata zargin cewa ya yi wa Peter Obi barazana, yana mai cewa babu wani abu daga cikin hirarsa da za ta nuna haka
  • Morka ya bayyana cewa zai miƙa takardun da suka ƙunshi barazanar ga hukumomin tsaro domin ɗaukar matakan kare rayuwarsa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kakakin jam’iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, ya bayyana cewa ya fuskanci barazanar kisa sakamakon kalamansa kan Peter Obi, na jam’iyyar LP.

Morka ya ce barazanar sun biyo bayan zargin da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023, Peter Obi ya yi cewa ya yi kalaman da su ka zama barazana ga rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Ganduje ya karbawa kakakin APC da za a 'kashe' fada, ya zafafa kalamai ga Obi

Peter
Kakakin APC ya ce ana barazana ga rayuwarsa Hoto: Peter Obj/Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Felix Morka, wanda ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi a shirin The Morning Show na Arise Television ranar Laraba ya kara da cewa yanzu haka ana barazana ga rayuwarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Morka ya ƙaryata zargin barazana ga Obi

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Morka ya musanta zargin Obi bayan wata hira da ya yi, a inda ya zargi tsohon ɗan takarar da wuce gona da iri wajen caccakar gwamnatin tarayya.

Ya ƙara da cewa;

“Ni, Felix Morka, ban yi wa Peter Obi barazana ba. Babu wani abu daga cikin abin da na faɗa a wannan hira da zai nuna haka, ko kaɗan.
“A matsayina na kakakin jam’iyyar APC, aiki na ne in bayyana gaskiya idan Obi ya fito a gidan talabijin na ƙasa kuma ya faɗi abubuwan da na ga suna gaskiya ba ne.”

"Ana yi mani barazana," Morka

Kakakin APC na kasa, Felix Morka ya ce an rubuta takardu sama da 400 na barazana, ciki har da kimanin 200 waɗanda suka yi barazanar kisa kai tsaye.

Kara karanta wannan

Menene gaskiyar labarin DSS sun kama Peter Obi? tsohon gwamnan ya fede gaskiya

Ya bayyana cewa zai miƙa waɗannan takardu ga hukumomin tsaro, ganin yadda wasu daga cikin masu barazanar su ka zayyana yadda za su kawar da shi.

Ya ce;

“Daga cikin waɗannan saƙonnin, wasu sun bayyana yadda za su cutar da ni—sun yi barazanar harbi na, yanke kaina, da kuma aikata wasu abubuwa masu ban tsoro.
"Wannan ba magana ba ce kawai. Har ma an yi barazana kai tsaye ga wasu daga cikin iyalina. Waɗannan barazanar ba su yi kama da rashin tabbas ba, sun ba da bayani dalla-dalla.”

Morka zai dangana da jami'an tsaro

Mista Morka ya ce Peter Obi ya na sane da cewa babu wani ɓangare na martanin da ya yi masa da ke zama barazana, saboda haka zai mika batun ga jami'an tsaron ƙasar nan.

Ya ce;

“Waɗanda suke aikata waɗannan barazanar suna yin haka ne da kansu, amma na tabbata hukumomin tsaro za su yi aiki da gaggawa don ganin an hukunta su.”

Kara karanta wannan

Shugaban NYSC ya fadi lokacin fara biyan masu yi wa kasa hidima N77,000

Atiku ya yi tir da barazana ga Obi

A baya, kun ji cewa Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu da jam'iyyar APC kan barazanar da aka ce an yi wa Peter Obi, yana mai cewa hakan ya saba dimokuradiyya.

Atiku ya bayyana cewa kalaman kakakin APC, Felix Morka, da suka yi wa Obi suna nuna rashin yarda da muhawara mai amfani, tare da nuna alamun kama-karya a siyasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.