Tsohon Shugaban AMAC Ya Sauya Sheƙa zuwa APC, Ya Shiga Taƙarar Gwamna
- Tsohon shugaban ƙaramar hukumar kwaryar birnin Abuja (AMAC), Prince Nicholas Ukachukwu ya sauya sheka zuwa APC a Anambra
- Ukachukwu ya kuma bayyana cewa ya amince da kireye-kirayen da ake masa na tsayawa takarar gwamnan Anambra a zaɓen da za a yi a 2025
- Ya ce idan mutane suka zaɓe shi ya hau kan karagar mulki, zai magance matsalar tsaro, talauci da sauransu cikin watanni uku kaɗai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra - Tsohon shugaban karamar hukumar birni ta babban birnin tarayya Abuja (AMAC), Prince Nicholas Ukachukwu ya koma jam'iyyar APC.
Tsohon ciyaman ɗin AMAC wanda ake kira da Ikukuoma ya ayyana shirinsa na neman takarar gwamnan jihar Anambra a zaɓen da za a yi a 2025.
Tribune Nigeria ta ce an gudanar da taron sauya sheƙarsa zuwa APC ne a gidansa da ke Osumenyi, ƙaramar hukumar Nnewi ta Kudu a Anambra jiya Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya samu tarba a hukumance daga shugaban jam’iyyar APC na gundumar Osumenyi, Hon. Ikechukwu Onyeka, tare da sauran shugabanni.
Tsohon shugaban AMAC zai nemi takara
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, Ukachukwu ya nuna farin cikinsa da shiga APC domin haɗa Anambra da cibiyar gwamnati (Abuja).
“Na amince da shiga jam’iyya mai mulki ne domin tsayawa takarar gwamna bayan kiraye-kiraye da kuma lallashin da wasu mutane, kungiyoyin farar hula, da kungiyoyin siyasa suka yi mani," in ji shi.
Ƙungiyoyin da ya ce sun nemi ya tsaya takara sun haɗa da kungiyar SOFIG, Ikemba Frontiers, gidauniyar Ifeanyi Ubah da ƙungiyar mata ta Golden.
Dalilin neman zama gwamnan Anambra
Ukachukwu ya ce:
"Zan nemi zama gwamnan Anambra ne domin samar da nagartaccen shugabanci wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara a Najeriya.
"Zan yi takara domin na sa Anambra ta zama wuri mafi kyau ga duk ‘yan Najeriya. Tun daga 1999 nake a harkar siyasa, don haka ina da kwarewar da ake bukata domin jagorantar jihar nan.
"Na shirya tsaf domin ‘yantar da mutanena daga matsalolin rashin tsaro, talauci, yunwa, da wahalhalu da ke addabar jihar a karkashin gwamnatin Gwamna Chukwuma Charles Soludo na jam’iyyar APGA."
"Zan share hawayen Anambra" - Ukachukwu
Ɗan siyasar ya tabbatarwa al'umma cewa idan suka zane shi ya zama gwamnan Anambra ranar 8 ga watan Nuwamba, 2025, zai magance matsalolin da suka dame su cikin watanni uku.
"Idan na samu nasarar hawa mulki, zan warware dukkan matsalolin da suka addabi jama'a cikin watanni uku.
"Zan tafiyar mulkin Anambra kamar kasuwanci, shekaru huɗu sun ishe ni na kafa tarihin da ba za a manta da shi ba a jihar nan."
Tsohon shugaban PDP ya koma APC
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban PDP reshen jihar Abia da ke Kudu maso gabashin Najeriya ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.
Sanata Emma Nwaka ya ɗauki wannan mataki nw kimanin watanni shida bayan ya fice daga PDP, lamarin da ya ba magoya bayan abokan adawarsa mamaki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng