Ana Hasashen Hadakar Adawa, El Rufai Ya Gana da Hamza Al Mustapha da Jigon PDP

Ana Hasashen Hadakar Adawa, El Rufai Ya Gana da Hamza Al Mustapha da Jigon PDP

  • Yayin da ake ta cigaba da hasashe kan hadakar jam'iyyun adawa a Najeriya, manyan yan siyasa sun gana a birnin Tarayya Abuja
  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya gana da Manjo Hamza Al-Mustapha da shugaban jam'iyyar SDP da jigon PDP
  • Rahotanni sun tabbatar da ganawar ba ta rasa nasaba da halin da kasa ke ciki da kuma shirye-shiryen jam'iyyun adawa kan zaben 2027

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi wata ganawa ta musamman da shugaban jam'iyyar SDP.

Tsohon gwamnan ya gana da tsohon dogarin marigayi Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha da kuma jigon PDP, Segun Showunmi.

El-Rufai da Hamza Al-Mustapha sun gana da wasu yan adawa a Abuja
Nasir El-Rufai ya gana da Major Hamza Al-Mustapha da wasu jiga-jigan yan adawa. Hoto: @SegunShowunmi.
Asali: Twitter

Jam'iyyun adawa na haɗaka kan zaben 2027

Shugaban kungiyar yan adawa, NOM, Otunba Segun Showunmi shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X a yau Talata 7 ga watan Janairun 2025.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa Kwankwaso shagube, ya yi barazanar kwace Kano a zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne yayin da ake ta hasashen jam'iyyun adawa na shirye-shirye mai ƙarfi domin tunkarar zaben 2027.

Mafi yawan masu neman hadakar na kokawa kan salon mulkin shugaba Bola Tinubu da suke ganin ya gaza bayan jefa al'umma cikin halin kunci da ya yi.

Daga cikin wadanda ake hasashen za su yi hadakar da ke gaba-gaba akwai dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar da na LP, Peter Obi.

Sai dai jagoran jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Kwankwaso ya yi fatali da maganar, ya ce babu wata yarjejeniya da suka yi musamman kan karba-karba.

El-Rufai ya gana da Al-Mustapha da jigon PDP

Wani babba a PDP, Otunba Segun Showunmi ya ce sun yi ganawar domin gaisawa da kuma tatttaunawa musamman kan halin da kasa ke ciki.

Showunmi ya ce yayin ganawar, sun yi duba kan karfin jam'iyyun adawa musamman game da zaben 2027 da ke tafe.

Kara karanta wannan

LND: Ana shirin kafa sabuwar jam'iyya domin buga APC da kasa a 2027

Wannan ganawa ta sake rura wuta kan zargin da ake yi cewa El-Rufai yana kokarin barin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

"Dole ne a tashi da wuri"
"Shugaban Jam’iyyar SDP, Girma Shehu Gabam ya kira taro na musamman da Nasir El-Rufai da Manjo Hamza Al-Mustapha da Otunba Segun Showunmi."
"An shirya wannan taron ne domin gaisawa da tattaunawa kan halin da ake ciki a bangaren adawa da ci gaban dimokuradiyya a Najeriya."

- Cewar Otunba Segun Showunmi

Atiku ya shiga fadan Obi da Tinubu

A baya, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya shiga rigima tsakanin gwamnatin Bola Tinubu da Peter Obi kan zargin yi masa barazana.

Atiku ya ce maganganun kakakin jam'iyyar APC, Felix Morka a kan Peter Obi, sun nuna wata alama ta rashin yarda da 'yancin masu adawa wanda ke kawo tarnaki ga dimukraɗiyya.

Ya ce kalaman da suka nuna Obi ya "ketare iyaka" sun bayyana rashin girmamawa ga dimukradiyya da muhimmancin muhawara mai amfani da kuma yancin fadan albarkacin baki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.