Gwamnan Bauchi Ya Ki Janye 'Barazana' ga Tinubu, Ya Sake Martani Mai Zafi
- Gwamnatin Bauchi ta karyata ikirarin cewa gwamna Bala Mohammed ya yi barazana ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- Gwamna Bala Mohammed ya bayyana cewa ya yi gargadi ne kawai domin tabbatar da adalci wajen aiwatar da kudirin gyaran haraji
- Wani mazaunin karamar hukumar Darazo, Umar Musa ya bayyanawa Legit cewa lallai gwamnan yana magana ne a kan ra'ayinsu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta karyata ikirarin fadar shugaban kasa na cewa gwamna Bala Mohammed ya ce ana adawa da Arewa kan kudirin haraji.
A wata sanarwa da aka fitar daga gidan gwamnatin jihar Bauchi, an bayyana cewa gwamna Bala Mohammed yana da burin kare muradun talakawa ne kawai ta hanyar ganin an samu adalci.
Sanarwar da aka wallafa a shafin gwamnan na Facebook ta ce ana son bata sunan Bala Mohammed ne saboda shi dan jam’iyyar PDP ne ba tare da duba ga gaskiyar lamarin ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matsayar gwamnan Bauchi kan haraji
Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewa gwamna Bala Mohammed ya yi gargadi kan yadda kudirin haraji zai kara wa talakawa wahala.
“Ya dace a fahimci cewa gargadin da gwamnan ya yi ba ya nufin yin barazana ga gwamnatin tarayya.
An yi shi ne domin tabbatar da cewa an sauya fasalin dokar haraji cikin adalci da daidaito ga kowane bangare,”
- Gwamnatin Bauchi
Gwamnan ya ce akwai gwamnonin APC da dama da suka caccaki kudirin harajin amma sai ka ware shi da martani wanda alama ke nuna saboda yana PDP ne.
Wa ye bai son a tatttauna kudirin haraji?
Gwamnatin Bauchi ta yi zargin cewa gwamnatin tarayya ba ta yi shawarwari na hakika ba kafin gabatar da kudirin harajin ga majalisar dokoki.
Ta kara da cewa kwamitin tattalin arzikin kasa ya bayar da shawarar a sake nazarin kudirin harajin, amma gwamnatin tarayya ta yi kunnen uwar shegu.
Gwamnatin jihar Bauchi ta ce rashin shawarwarin ya nuna rashin kula ga lamuran da za su inganta rayuwar al’umma.
Legit ta tattauna da dan jihar Bauchi
A martanin da ya yi, gwamnan ya ce mutanen jihar Bauchi suna goyon bayansa a kan matsayarsa, wanda kuma wani mazaunin jihar Bauchi ya tabbatarwa Legit hakan.
Umar Musa da ke zaune a karamar hukumar Darazo ya bayyanawa Legit cewa gwamnan ya hango musu matsala ne kan kudirin kuma suna goyon bayansa.
Sanata Akpabio ya goyi bayan Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya ce yana goyon bayan tsare tsaren Bola Tinubu.
Godswill Akpabio ya bayyana cewa shugaban kasar ya samu Najeriya a wani irin hali maras kyau a lokacin da ya karbi mulki a shekarar 2023.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng