"Za Mu Hargitsa APC," Jigo a Kano Ya Ce za Su Bijirewa Shugabancin Ganduje

"Za Mu Hargitsa APC," Jigo a Kano Ya Ce za Su Bijirewa Shugabancin Ganduje

  • Jigo a APC reshen jihar Kano, AbdulMajid Danbilki Kwamanda ya nemi matasa su tashi don adawa da jagorancin jam'iyyar
  • Kwamanda ya ce jagorancin Abdullahi Umar Ganduje a kasa da ta Abdullahi Abbas a Kano, babbar annoba ce a siyasa
  • Ya yi alkawarin jagorancin tafiyar da za ta hargitsa jam'iyyar har sai an tumbuke shugabancin mutanen biyu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Kusa a jam'iyyar APC a Kano, AbdulMajid Danbilki Kwamanda ya yi zargin cewa shugabancin Abdullahi Abbas da Abdullahi Ganduje annoba ne ga APC.

Ya bayyana haka ne a Kano, yayin da ya ke zargin cewa jagorancinsu ya na haddasa rashin adalci da watsi da bukatun 'yan jam'iyya da.

Jihar
Jigon APC ya fusata da salon mulkin Ganduje Hoto: AbdulMajeed Danbilki Kwamanda/Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

A bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, AbdulMajid Danbilki Kwamanda ya kara da zargin Ganduje, wanda shi ne shugaban jam'iyyar na kasa da aikata ba dai-dai ba.

Kara karanta wannan

"Carter mai son cigabanmu ne," Tinubu ya yi jimamin mutuwar tsohon shugaban Amurka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin boren jigon APC ga Ganduje

Kwamanda, wanda masoyi ne ga tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya zargi Abdullahi Umar Ganduje da jefa jam'iyya a aljihunsa.

Ya kara da cewa;

"Za ka ga duk wanda su ke nemo wa mukami, billahillazi, yadda ya ke so haka zai juya su. Idan ba haka ba, mai yasa ba a ba Murtala Sulen Garo mukami ba? Ai ya kamata mukamin da aka bawasu mutane, ya kamata a ce shi za a ba. A matasa akwai wanda ya ke taimakon jam'iyyar APC irin Murtala?

Kusan APC zai tattaro kan 'yan jam'iyya

AbdulMajid Danbilki Kwamanda ya yi barazanar cewa zai tattaro kawunan wasu daga cikin 'yan jam'iyyar APC da ke Kano domin a yi bore ga shugabancin Abdullahi Umar Ganduje.

Ya kara da cewa;

Ganduje ya iya munafunci a siyasa, ya iya kurde-kurde a siyasa, ya iya kwantar da hankali don ya biya bukatar kansa.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Jonathan ya soki El Rufa'i kan zargin kabilanci a gwamnatin Tinubu

Annoba ne a siyasa, kuma a APC annoba ne, sai mun tumbuke shi. Kuma za mu fito, za mu yi duk abin da tsarin mulki ya ba mu a jam'iyya, Wallahi za mu bijere musu."

"Ka dawo APC," Kwamanda ga Sanata Kawu

A wani labarin, mun ruwaito cewa jagora a jam'iyyar APC a Kano, AbdulMajid Danbilki Kwamanda ya nemi Sanatan NNPP, Kawu Sumaila da ya dawo cikin jam'iyyar.

Yayin da ya ke yabon nagartar Kawu, Kwamanda ya kara da cewa su na da tabbacin zai iya zama gwamnan Kano matukar ya amince a fito wa takara a inuwarta a zaben 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.