PDP Ta Ƙara Nutsewa cikin Rikici, Sabon Sakataren Jam'iyyar na Kasa Ya Kama Aiki

PDP Ta Ƙara Nutsewa cikin Rikici, Sabon Sakataren Jam'iyyar na Kasa Ya Kama Aiki

  • Hon. Sunday Udeh-Okoye ya kama aiki a matsayin sabon sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara
  • Sabon sakataren ya dura sakatariyar PDP da ke Wadata Plaza, aka ji yana cewa ya fara aiki daga ranar 30 ga watan Disamba, 2024
  • Tun farko dai kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Enugu ta tsige Samuel Anyanwu daga matsayin sakataren PDP tare da maye gurbinsa da Udeh-Okoye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Sabon sakataren PDP na kasa, Hon. Sunday Udeh-Okoye, ya kama aiki a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.

Ya bayyana cewa yana aiki ne da hukuncin kotun daukaka kara, wanda ya tabbatar da shi a matsayin wanda zai maye gurbin Sanata Samuel Anyanwu.

Hon. Sunday Udeh-Okoye.
Sabon sakataren PDP na kasa, Udeh-Okoye ya kama aiki bayan hukuncin kotu Hoto: Hon. Sunday Udeh-Okoye
Asali: Facebook

Sabon sakataren PDP ya kama aiki a Abuja

Leadership ta gano cewa Udeh-Okoye, tsohon shugaban matasan PDP na kasa, ya fita aiki a karon farko a sakatariyar jam’iyyar da ke Wadata Plaza a jiya Litinin.

Kara karanta wannan

"Wuce gona da iri," Dattawan Arewa sun ce a biya diyyar wadanda sojoji suka hallaka a Sakkwato

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi, sabon sakataren ya ce tuni suka miƙawa hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta watau INEC hukuncin da kotu ta yanke kuma ta karɓa.

A ranar Talatar da ta gabata ne PDP ta karɓi kwafi kuma ta amince da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na naɗa Udeh Okoye a matsayin sabon sakatare.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba a ranar Juma’a ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta samu hukuncin kuma za ta bi umarnin kotu.

Sai dai Sanata Anyanwu ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun koli amma har yanzu bai samu umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin kotun ba.

Sabon sakataren ya yi jawabi a karon farko

"Abin da ya sa kuka gan ni a nan shi ne aiki, na shiga ofis bisa dogaro da hukuncin kotun ɗaukaka kara da ke zama a Enugu, wadda ta tsige Anyanwu ta ɗora ni a kujerar sakataren PDP na ƙasa.

Kara karanta wannan

Harin bam a Sokoto: PDP ta jajantawa iyalai, ta ba gwamnati shawara

"Na zo yau 30 ga watan Disamba, 2024 domin na fara aiki kuma na duba yanayin da sakatariya take ciki, na tarar ma'aikata sun tafi hutun kirismeti, za su dawo ranar 13 ga watan Janairu.
"Ina kuma godiya ga ƙungiyar gwamnoni da suka ba ni goyon baya, ƙungiyar tsofaffin ministoci, majalisar amintattau (BOT), ’yan jam’iyya, da jagororin PDP na shiyyata, wadanda suka zabe ni."

- In ji sabon sakataren PDP na kasa, Hon. Sunday Udeh-Okoye.

Jigon PDP ya hango karyewar APC a 2027

A wani labarin kun ji cewa wani jigon PDP ya bayyana shirinsu na kayar da shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 mai zuwa.

Mai magana da yawun kungiyar matasan PDP, Dare Glintstone Akinniyi ya ce ƴan Najeriya sun gaji da karerayin APC, cikin sauki za su karbe mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262