APC Ta Fara Fargabar Wani Gwamna a Arewa na Iya Ficewa daga Jam'iyya

APC Ta Fara Fargabar Wani Gwamna a Arewa na Iya Ficewa daga Jam'iyya

  • Kungiyar APC a Arewa ta Tsakiya ta gargaɗi sakataren gwamnatin tarayya watau SGF, George Akume ya canza salonsa na siyasa
  • Shugaban kungiyar, Alhaji Saleh Zazzaga ya ce idan har gwamnan Benuwai, Hyacinth Alia ya bar APC to laifin Sanata Akume ne
  • George Akume ya yi fatali da zargin, ya ce babu kanshin gaskiya a kalaman kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jam'iyyar APC ta ja hankalin sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume kan ya gyara takun siyasarsa a jihar Benuwai.

Ƙungiyar ƴan APC a Arewa ta Tsakiya ta bukaci Akume ya ƙauracewa duk wani abu na tsangwama da ka iya tilastawa Gwanna Hyacinth Alia na Benuwai ficewa daga jam'iyyar.

Gwamna Alia da Akume.
Kungiyar APC ta gargaɗi Akume ya guji matsawa Gwamna Alia lamba a jihar Benue Hoto: Fr. Hyacinth Lormem Alia
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kungiyar ta fitar bayan wani taro da ta gudanar a Abuja ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Zamfara ya fadi lokacin da matsalar tsaro za ta kare, ya jero dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC na fargabar Gwamna Alia ya canza sheƙa

Kungiyar APC a Arewa ta Tsakiya ta nuna damuwa kan yarfe da cin mutuncin Gwamna Alia da wasu mutane ke yi a kafafen sada zumunta.

A sanarwar mai ɗauke da sa hannun shugaban kungiyar, Alhaji Saleh Zazzaga ta gargadi Akume kan yunkurin ɓata Alia wanda ka iya ruguza APC a zaɓen 2027 a jihar.

Saleh Zazzaga ya ce jam'iyyar APC ba za ta lamunci sake rasa jihar Benuwai ba kamar yadda ta faru a baya lokacin da Gwamna Samuel Ortom ya bar jam'iyyar.

Akume na neman naƙasa APC a Benue?

Zazzaga ya ce matuƙar Gwamna Alia ya yanke shawarar ficewa daga APC zuwa wata jam'iyya, ba laifin kowa ba ne illa laifin sakataren gwamnatin tarayya.

Shugaban ƙungiyar ya ce:

"Idan tarihi ya maimaita kansa, Gwamna Alia ya koma wata jam'iyyar kamar yadda Samuel Ortom ya ci zaɓe a inuwar APC amma ya koma PDP, to ba laifin kowa ba ne illa Akume."

Kara karanta wannan

APC ta samu tagomashi, mataimakin shugaban majallisa ya tarbi 'yan adawa 3,000

"APC ba za ta lamurci rasa jihar Benuwai ba kamar yadda ba za ta rasa Gwamna Alia ba. Ya kamata sakataren gwamnatin tarayya da karnukansa su bar Alia ya yi aikin da ke gabansa."

Akume ya musanta ɗaukar nauyin ƴan midiya

Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, mai magana da yawun Akume, Terrence Kuanum, ya yi watsi da ikirarin kungiyar a matsayin mara tushe.

"Babu gaskiya a ikirarin cewa SGF ne ya ɗauki nauyin sojojin midiya suke ta zagin Gwamna Alia."

Gwamna ya faɗi dalilin zuwansa taron ɗan LP

Kun ji cewa Gwamna Francis Nwifuru na APC ya halarci taron raba kayan tallafi wanda ɗan Majalisar wakilai na jam'iyyar LPya shirya a jihar Ebonyi.

Zuwa gwamnan na APC wurin ya ɗauki hankalin jama'a musamman saboda saboda ba jam'iyyarsu ɗaya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262