Gwamnan APC Ya ba Mutane Mamaki, Ya Halarci Taron Ɗan Majalisar LP

Gwamnan APC Ya ba Mutane Mamaki, Ya Halarci Taron Ɗan Majalisar LP

  • Gwamnan jihar Ebonyi ya jagoranci kusoshin APC sun halarci taron rabon tallafi na ɗan majalisar tarayya na jam'iyyar LP
  • Farancis Nwifuru ya bayyana cewa ya halarci taron ne saboda siyasa ba gaba ba ce kuma ɗan majalisar abokinsa ne
  • Ya buƙaci ɗan Majalisar ya dawo APC tun kafin lokaci ya kure domin idan zaɓe ya zo, ba zai yi masa yakin neman zaɓe ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ebonyi - Gwamna Francis Nwifuru na Ebonyi ya bayyana cewa ya halarci taron da wani dan majalisar wakilai na LP daga jihar ya shirya domin siyasa ba gaba ba ce.

An ga Gwamna Nwifuru na jam'iyyar APC a wurin taron rabon tallafi wanda mamba mai wakiltar Ohaoazara/ Onicha/ Ivo a Majalisar wakilai ta ƙasa ya shirya.

Gwamna Francis Nwifuru.
Gwamnan Ebonyi ya halarci taron rabon tallafi na ɗan majalisar jam'iyyar LP Hoto: Francis Nwifuru
Asali: Twitter

Gwamna Nwifuru ya halarci taron ɗan LP

Kara karanta wannan

APC ta fara fargabar wani gwamna a Arewa na iya ficewa daga jam'iyya

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ɗan majalisar, Hon. Nkemkanma Kama na LP ya shirya taron rabon tallafin ne ranar Litinin a Ishiagu, karamar hukumar Ivo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi a wurin, Gwamna Nwifuru na APC ya ce ya zo wurin taron ne domin ya kara fito da ma'anar cewa siyasa ba gaba ba ce.

Dalilin gwamnan APC na zuwa taron

"Kamata ya yi Hon. Kama ya zama maƙiyi na saboda ɗan wata jam'iyya ne daban to amma ga shi ya zama abokina. Ku sani zaɓe ya wuce, batu ake yi na shugabanci."
"Wannan ya sa na tattaro shugabanni APC muka taho nan har da shugaban jam'iyya na jihar Ebonyi. Duk taron da na je ko da raɗin suna ne za ka ga Hon. Kama a wurin.
"Na ba shi shawara ya shigo APC tun kafin mu rufe ƙofa saboda idan zaɓe ya zo, ɗan jam'iyya ta kaɗai zan yi wa kamfe. Ka tabbata ka ba ƴan APC kayan nan don idan ka shigo su faɗi alheri a kanka."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi wankin babban bargo ga gwamnan Bauchi kan haraji

- Gwamna Nwifuru.

Kayayyakin da ɗan majalisar ya rabawa mutane a taron sun haɗa da Keke-Nafef, babura, injinan nika, kekunan dinki, injinan gyaran gashi da sauran su.

Gwamnan Ebonyi ya ba ciyamomi shawara

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Nwifuru ya nuna damuwan kan yadda ciyamomin ƙananan hukumomi suka rike albashin ma'aikatansu.

Gwamnan wanda ya nuna takaicinsa a fili, ya buƙaci ciyamomin su yi murabus idan sun san ba za su iya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262