'Yadda Saraki Ya Yaudare Ni bayan Masa Gata': Sanata Ndume Ya Bude Aiki, Ya Fadi Shirinsa

'Yadda Saraki Ya Yaudare Ni bayan Masa Gata': Sanata Ndume Ya Bude Aiki, Ya Fadi Shirinsa

  • Sanata Mohammed Ali Ndume ya bayyana yadda aka dakatar da shi daga Majalisar Dattawa ta 8 ba tare da albashi ba
  • Sanata Ndume ya zargi tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, da cin amanarsa a lokacin da ya zama Shugabanta
  • Sanatan ya nuna damuwa kan yadda matsalar talakawa ke cigaba da tabarbarewa duk da kokarinsa wajen tallafa musu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Borno - Sanata Mohammed Ali Ndume, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu, ya bayyana yadda aka ci amanarsa a Majalisar Dattawa.

Sanata Ndume ya ce an dakatar da shi daga Majalisar Dattawa ta 8 ba tare da albashi ba.

Ndume ya fadi yadda Saraki ya yaudare shi
Sanata Ali Ndume ya koka kan butulci da Bukola Saraki ya yi masa. Hoto: Mohammed Ali Ndume.
Asali: Facebook

'Yadda Saraki ya ci amana ta' - Ndume

Da yake magana da DW Hausa, Ndume ya bayyana yadda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ci amanarsa duk da goyon bayan da ya ba shi.

Kara karanta wannan

Rarara ya yi wa shugaban Nijar wankin babban bargo kan zarginsa, ya tona asiri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanatan ya kuma ce an cire shi daga matsayin mai tsawatarwa na Majalisar Dattawa ta 10 saboda fadan gaskiya.

“An cire ni a matsayin shugaban masu rinjaye kuma daga baya aka dakatar da ni tsawon watanni takwas ba tare da albashi ba."
"Wannan abu ya dame ni kwarai saboda mu ne muka taka rawa wajen tabbatar da Saraki a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa, amma ya ci amanar mu."

- Ali Ndume

Ndume ya damu kan rayuwar talakawan Najeriya

Ndume ya ce an sake cire shi daga matsayin mai tsawatarwa saboda ya fadi gaskiya, amma ya ce yanzu wannan abu ya zama tarihi.

Sanatan ya bayyana damuwarsa kan yadda matsalar halin da talakawa ke ciki ya ke cigaba da tabarbarewa duk da kokarinsa wajen tallafa musu.

Garambawul: Ndume ya ba Tinubu shawara

Kun ji cewa Sanata Mohammed Ali Ndume ya yabawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa garambawul din da ya yi a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Rashin nadamar cire tallafin fetur da abubuwa 3 da Tinubu ya fada a kan manufofinsa

Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu ya buƙaci Tinubu ya sake haska majalisar zartaswa domin akwai sauran ministocin da ya kamata a kora.

Ya kuma ba shugaban ƙasar shawarar ya haɗa taron tattalin arziki domin lalubo mafita da wannan halin da ƙasa ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.