2027: Ana Zargin Gwamna da Balle Hotunan Sanata da Rikicin APC Ya Kazanta
- Ana hasashen rigimar siyasa ta kunno kai a jihar Kwara bayan cire allunan tallan Sanata Saliu Mustapha da aka girke a wurare daban-daban
- Sanatan da ke wakiltar Kwara ta Tsakiya ya yi kyautar ₦500m don gina wurin taro a fadar Sarkin Ilorin saboda gudanar da taruka
- Masana siyasa sun danganta cire allunan tallan da rikicin siyasar cikin gida na APC yayin da aka fada maganar zabukan 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kwara - An cire allunan tallan Sanata Saliu Mustapha da aka girke a wurare daban-daban a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ranar Juma’a.
Sanatan, wanda shi ne Turakin Ilorin, ya sanar da kyautar ₦500m don gina wurin taro a fadar Sarkin Ilorin, don amfanin jama'a.
Ana zargin rikicin APC ya munana a Kwara
Punch ta ce cire allunan bai rasa nasaba da rikicin cikin gida na APC yayin da ake shirin zaben 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Allunan tallan sun kunshi saƙon taya murna ga Kiristoci na bikin Kirsimeti, wadanda aka girke su a wurare kamar kan hanyar Unity da tashar jirgin sama.
Wani bidiyo da ya bazu a Facebook ya nuna wani mutum yana cire allunan tallan da suka ƙunshi saƙon Kirsimeti na Sanata Mustapha, cewar The Nation.
Masana siyasa sun danganta cire allunan da rikicin siyasar cikin gida na APC yayin da ake shirin zabukan majalisar dattawa da gwamna na 2027.
Sanatan ya ƙaryata jita-jitar rigimaraa da gwamna
Kakakin Sanata Mustapha, AbdulKareem Alabi, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya musanta cewa gwamnatin jihar ta da hannu.
"Yan daba ne suka cire allunan tallan, ba gwamnatin jihar ba, hukumomi na cigaba da bincike."
- Cewar sanarwar
Wasu mazauna birnin sun yi kira da a tabbatar da zaman lafiya a Kwara, saboda hakan shi ne komai da ke kawo cigaban ƙasa.
Tsohon kwamishina ya rasu a Kwara
Kun ji cewa tsohon kwamishinan yaɗa labarai a jihar Kwara, Alhaji Abdulrahim Adisa ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 91 a duniya.
Kungiyar ƴan jarida (NUJ) reshen jihar Kwara ta tabbatar da rasuwar a wata sanarwa da ta fitar ta hannun sakatarenta.
Asali: Legit.ng