Hadimin Tinubu Ya Roƙi Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Ya Koma Jam'iyyar APC
- Hadimin shugaban ƙasa Bola Tinubu ya roƙi tsohon takarar gwamnan jihar Bayelsa a inuwar LP, Udengs Eradiri ya dawo APC
- Tokoni Peter Igoin ya roki ɗan siyasar ne a lokacin da ya kai masa ziyara har gida kwanakin kaɗan bayan ya fice daga LP
- Ya ce shugaba Tinubu ya shirya ceto Najeriya daga halin da ta tsinci kanta, sannan ya na mutunta matasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bayelsa - Mai ba shugaban ƙasa, Bola Tinubu shawara kan harkokin fasahar sadarwa (ICT), Tokoni Peter Igoin ya fara zawarcin tsohon ɗan takarar gwamna a Bayelsa.
Peter Igoin ya roƙi tsohon ɗan takarar gwamnan Bayelsa a inuwar jam'iyyar LP, Udengs Eradiri ya dawo APC mai mulkin Najeriya.
Hadimin Tinubu ya ziyarci tsohon ɗan takara
The Nation ta ruwaito vewa hadimin Tinubu ya yi wannan rokon ne da ya ziyarci Eradiri, dan kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya (NSE), a gidansa da ke kauyen Azikoro, Yenagoa, ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan fitar da ɗan takarar gwamnan ya yi daga jam'iyyar LP, inda ya ce zai nemo wata jam'iyyar da za ta ba shi damar hidimtawa al'umma.
Yayin da ya kai masa ziyara tare da wasu makunsanta da matasan karamar hukumarsa watau Kolokuma-Opokuma, Peter Igoin ya ce Tinubu ya shirya gyara Najeriya.
Ya kuma yaba da tsare-tsaren da Tinubu ya bullo da su fannin ICT, inda ya ce tuni suka fara haifar da sakamako mai kyau kuma za su rage ƙuncin rayuwa nan gaba.
Ya fara zawarcin ɗan takarar gwamna
Hadimin Tinubu ya ƙara da jaddada kudirin shugaban kasa kan batun ci gaban matasa da kuma yin aiki tare da masu basira, masu hankali kamar Eradiri.
"Ba wai umarni nake baka ka dawo APC ba, ina roƙonka da ka shigo jam'iyyarnu domin mu haɗu mu marawa shugaba Tinubu baya saboda ya nuna zai iya ceto Najeriya."
"Shugaban ƙasarmu yana mutunta matasa kuma yana samar masu da damarmaki, zan yi farin ciki idan ka dawo APC mu haɗu mu mara masa baya.
- Tokoni Peter Igoin.
Tinubu ya samu goyon baya a Arewa
Kun ji cewa kungiyar magoya bayan APC a Arewa ta Tsakiya ta jaddada goyon bayansu ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban ƙungiyar, Saleh Zazzaga ya bayyana cewa za su sake zaɓen Tinubu ya zarce zango na biyu a zaɓen 2027.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng