Tsohon Ministan Sadarwa, Sheikh Pantami Ya Yi Magana kan Yiwuwar Ya Fito Takara a 2027

Tsohon Ministan Sadarwa, Sheikh Pantami Ya Yi Magana kan Yiwuwar Ya Fito Takara a 2027

  • Nafiu Usman Bello, wanda ya taso tun daga Gombe zuwa Abuja a babur ya roki Sheikh Isa Pantami ya fito takarar gwamna a 2027
  • Mutumin wanda ya miƙa wanann roko a madadin wata kungiya mai zaman kanta, ya ce suna fatan Pantami ya kawo sauyi a Gombe
  • A nasa jawabin, tsohon ministar sadarwa, Malam Isa Pantami ya ce zai sanar da al'ummar Gombe shawarar da ya yanke a lokacin da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wata kungiya mai zaman kanta mai suna ‘Gombe State Promoters Forum in Broadcasting Media’ ta roki Sheikh Isah Pantami ya fito takara a 2027.

Ƙungiyar ta bukaci tsohon ministan sadarwa, Sheikh Farfesa Isah Ali Pantami ya tsaya takarar gwamnan jihar Gombe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Duk da rashin tsaro, malami na tafiyar 25km a keke domin koyarwa a Katsina

Farfesa Pantami da Nafiu.
Farfesa Isa Ali Ibrahim.Pantami ya ce zai sanar da matsayarsa kan yiwuwar tsayawa takarar gwamnan Gombe Hoto: Professor Isa Pantami
Asali: Facebook

Shugaban ƙungiyar, Nafiu Usamn Bello ne ya isar da wannan saƙo yayin da ya ziyarci Pantami a ofishinsa da ke Abuja, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An roki Pantami ya fito takarar gwamna

Nafiu ya kai wa Pantami ziyara ne bayan kammala tafiyar kimanin kilomita 562 a Babur daga Gombe zuwa Abuja domin rokon fitaccen malamin ya tsaya takara.

"A madadin kungiyarmu ina kira gareka da ka tsaya takarar gwamnan Gombe a 2027 don ci gaba da ayyukan alheri da ka saba da kuma kawo sauyi a jihar kamar yadda ka yi a ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani."

A nasa jawabi, Farfesa Pantami ya yabawa kungiyar da Nafiu bisa ziyarar da suka kawo masa daga jihar Gombe zuwa Abuja.

Pantami ya yi magana kan takara a 2027

Fitaccen malamin Sunnah ya bayyana cewa ba wannan ne karon farko ba, a akwai baya wasu kungiyoyi sun bukaci ya nemi takarar gwamnan Gombe.

Kara karanta wannan

"Ku ƙara imani da Allah SWT," Gwamna ya yi magana bayan gobara ta laƙume miliyoyin Naira

Malam Pantami ya shaidawa Nafiu wanda ya share doguwar tafiya a babur dominsa cewa zai sanar da al'ummar Gombe shawarar da ya yanke a lokacin da ya dace.

"Ina godiya da wannan kokari da kuka yi da kuma al'ummar jihar Gombe da ke ganin na cancanta na tsaya takarar gwamna.
"Sai dai ba tun yau kaa fara kiran na nemi takara ba, kuma idan lokaci ya yi, za mu sanar da mutane shawarar da muka yanke."

- Sheikh Farfesa Isa Pantami.

Pantami ya yi magana kan kudirin haraji

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan sadarawa, Malam Isa Ali Pantami ya bukaci gwamnatin tarayya ta sake nazari kan kudirin dokar haraji.

Farfesa Pantami ya ce akwai wasu wurare a cikin kudirorin dojar huɗu da ke gaban Majalisa da ya kamafa gwamnati ta sake tunani a kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262