Abba Ya Nada Kwamishioni 6, Hadimin da Aka Tsige Zai dawo Gwamnati

Abba Ya Nada Kwamishioni 6, Hadimin da Aka Tsige Zai dawo Gwamnati

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa sunayen mutane shida zuwa majalisar dokoki domin tantancewa a matsayin kwamishinoni
  • Sunayen sun haɗa da tsohon shugaban ma'aikatar fadar gwamnatin jihar, Shehu Wada Sagagi da aka sauke a makon da ya wuce
  • Wannan matakin na zuwa ne bayan da gwamnan ya dawo daga tafiya kasashen waje tare da yin gyaran fuska a majalisar zartarwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya miƙa sunayen mutane shida zuwa majalisar dokokin jihar domin tantancewa a matsayin sababbin kwamishinoni.

Wannan matakin ya biyo bayan sauya wasu mukamai a gwamnatinsa, wanda ya fara aiwatarwa makon da ya gabata.

Abba Kabir
Abba ya tura sunayen kwamishinoni ga majalisa. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da hadimin mataimakin gwamnan jihar, Abduulahi Ja'en ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun shiga alhini, sun yi ta'aziyyar mutuwar mutane a hadarin jirgin Binuwai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta wallafa cewa sababbin kwamishinonin sun hada da:

1. Shehu Wada Sagagi

2. Dr. Dahiru Hashim

3. Ibrahim Wayya

4. Dr. Isma’il Dan Maraya

5. Gaddafi Shehu

6. Abdulkadir AbdulSalam

Kafin yanzu, Shehu Wada Sagagi shi ne Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, wanda ofishinsa aka soke makon da ya gabata.

Abba ya ce za a sha ayyuka a Kano

Abba Kabir ya nada kwamishinonin ne bayan dawowarsa daga tafiya zuwa ƙasashen waje, inda ya ce tafiyar ta kasance mai amfani tare da buɗe sababbin damammaki ga jihar Kano.

Gwamnan ya wallafa a Facebook cewa yana fatan matakan da ya ɗauka za su kawo ci gaba mai amfani ga jihar da al’ummarta.

“Na dawo gida Kano, kuma an min tarba mai kayu bayan tafiya zuwa ƙasashen waje. Tafiyar ta samar da damammaki masu amfani ga jiharmu da al’ummarta.”

- Abba Kabir Yusuf

Abba ya ba Sani Danja mukami

Kara karanta wannan

Yaki da 'yan bindiga: Manyan Arewa sun halarci kaddamar da askarawa 5,000

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen jarumin Kannywood, Sani Musa Danja ya samu shiga gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf.

Rahoton Legit ya nuna cewa Abba Kabir Yusuf ya ba Sani Danja matsayin mai ba shi shawara na musamman a kan harkokin matasa da wasanni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng