Bayan Tinubu Ya Naɗa Shi Muƙami, Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Ya Fice daga PDP

Bayan Tinubu Ya Naɗa Shi Muƙami, Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Ya Fice daga PDP

  • Jam'iyyar PDP ta ƙara rasa babban jigonta a jihar Enugu mako guda bayan ƴar majalisar tarayya ta sauya sheka zuwa APC
  • Tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye a Majalisar wakilai, Hon. Toby Okechukwu ya fice daga jam'iyyar PDP
  • Ya tabbatar da hakan ne a wasiƙar da ya aike wa shugaban PDP na gundumarsa kwanaki kaɗan bayan samun muƙami a gwamnatin Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - Tsohon ɗan Majalisar wakilan tarayya, Hon. Toby Okechukwu ya tattara kayansa ya fice daga babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa watau PDP.

Okechukwu, tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye na Majalisar wakilai ya sanar da barin PDP ne a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 6 ga Disamba.

Toby Okechukwu
Tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye a Majalisar wakilai ya fice daga PDP Hoto: Hon. Toby Okechukwu
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa tsohon ɗan majalisar ya aika wasiƙar ne ga shugaban PDP na gumdumar Owelli/Amoli/Ugbo/Ogugu karamar hukumar Agwu a Enugu.

Kara karanta wannan

Ado Doguwa: 'Dan majalisa ya nemi afuwar APC kan yabon gwamnan PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Okechukwu ya wakilci mazaɓar Aninri/Awgu/Oji a Majalisar wakilai ta 7, 8 da kuma ta 9, watau sau uku yana cin zaɓen ɗan majalisa a mazaɓar.

Tsohon ɗan Majalisa ya fita daga PDP

A wasiƙar, ɗan siyasar ya miƙa godiyarsa ga jam'iyyar PDP bisa damar da ta ba shi har ya zama wakilin al'umma kuma ya yi wa mutanensa hidima.

Okechukwu ya ce:

"Na rubuto wannan wasiƙa ne domin sanar da ku na yi murabus daga PDP kuma ina godiya da damar da aka ba ni na wakilci mazaɓar Aninri/Awgu/Oji River a Majalisar tarayya ta 7,8 da 9."

Tsohon jigon PDP ya faɗi muƙaman da ya riƙe

Hon. Toby Okechukwu ya ƙara da bayyana irin gudummuwar da ya bayar wanda ya haɗa da aiki a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye a Majalisa.

Ya kuma riƙe shugaban kwamitin ayyuka da mataimakin shugaban kwamitin ɗa'a na Majalisar wakilan tarayya.

"Ina fatan nan gaba, za mu ci gaba da ba da gudummuwa daidai gwargwado domin inganta rayuwar al'umma," in ji shi.

Kara karanta wannan

An yi musayar yawu da wani ɗan Majalisar Tarayya ya sanar da komawa APC

Wannan mataki da tsohon ɗan majalisar ya ɗauka na zuwa ne bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shi a matsayin daraktan ayyuka na hukumar raya Kudu maso Gabas.

Ɗan Majalisar wakilai ya koma APC

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar LP ta kara yin babban rashi, ɗan Majalisar wakilai daga jihar Filato, Hon Dalyop Chollom ya sauya sheƙa zuwa APC.

Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙar da Chollom ya aiko a zaman ranar Talata, 10 ga watan Disambar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262