Baffa Bichi Ya Bayyana Dalilin Abba na Sauke Shi daga Sakataren Gwamnatin Kano

Baffa Bichi Ya Bayyana Dalilin Abba na Sauke Shi daga Sakataren Gwamnatin Kano

  • Dakta Baffa Bichi ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya ba shi na yi wa jihar Kano hidima kafin sauke shi
  • Tsohon sakataren gwamnatin ya bayyana cewa matsalar rashin lafiya ce ta sa aka sauke shi, kuma ya koyi darusa da dama
  • Baffa Bichi ya yabawa hadin kan jami’an gwamnati da al’ummar Kano, yana addu’ar zaman lafiya da fatan ci gaba mai dorewa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya magantu awanni bayan sauke shi daga mukamin sakataren gwamnatin jihar Kano (SSG).

A cikin wasikar da ya aikewa gwamnan Kano, Abba Yusuf, tsohon sakataren gwamnatin ya yi godiya da irin damar da aka ba shi na yiwa jihar hidima.

Baffa Bichi ya yi magana bayan sauke shi daga mukamin sakataren gwamnatin Kano
Baffa Bichi ya alakanta korarsa daga sakataren gwamnatin Kano da rashin lafiya. Hoto: bichibaffah
Asali: Instagram

"Abin da ya sa Abba ya sauke ni" - Baffa Bichi

Kara karanta wannan

Majalisar tarayya za ta binciki yadda gwamnatin Buhari ta kashe bashin $232m

A wasikar da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Dakta Baffa Bichi ya godewa Gwamna Yusuf bisa damar da ya ba shi na yin aiki a gwamnatinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da wasu ke ce-ce-ku-ce game da dalilin sauke shi daga wannan mukami, Baffa Bichi ya ce matsalar rashin lafiya ce ta sa aka sauke shi.

A cewar tsohon sakataren gwamnatin:

"Duk da yake wa’adina ya ƙare saboda dalilai na rashin lafiya, ina mai matukar godiya bisa irin gogewa da darussan da na koya yayin gudanar da aikina."

Baffa Bichi ya fadi darasin da ya koya

Dakta Bichi ya yabawa hadin kan jami’an gwamnati da al’ummar Kano a lokacin da ya ke ofis, yana fatan cigaban jihar.

Tsohon SSG ya ce kwarewar da ya samu yayin shugabancinsa na daya daga cikin abubuwan da zai rika tunawa tare da alfahari da su.

An sauke Baffa Bichi ne yayin da Gwamna Yusuf ke kokarin sake fasalin gwamnatinsa domin samun ingantaccen aiki a bangarori daban-daban.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa gwamnan Kano ya sauke sakataren gwamnati da wasu kwamishinoni 5

Dr. Bichi ya yiwa Kanawa fatan alheri

Masu sharhi sun yaba da wasikar Dakta Bichi, suna ganin wannan alama ce ta mutunci da sadaukarwa ga ci gaban Kano.

Dakta Baffa Bichi ya rufe wasikarsa da fatan alheri ga Kano, yana addu’ar zaman lafiya da cigaba mai dorewa ga al'ummar jihar.

Abin da ya sa Abba ya sauke Bichi

Tun da fari, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa babu wani laifi da Dakta Baffa Bichi ya yi aka sauke shi daga sakataren gwamnati.

Sanusi Bature Dawakin Tofa, mai magana da yawun Gwamna Abba Yusuf, ya ce an sauke Bichi da sauran mutane shida saboda kawo sauyi mai inganci a gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.