'Dan Takarar Gwamna da Mataimakinsa Sun Bar Jam'iyyar LP bayan Ficewar 'Yan Majalisa

'Dan Takarar Gwamna da Mataimakinsa Sun Bar Jam'iyyar LP bayan Ficewar 'Yan Majalisa

  • Guguwar sauya sheƙa ta sake faɗawa kan LP yayin da ɗan takararta na gwamnan jihar Bayelsa ya sanar da ficewars daga jam'iyyar
  • Udengs Eradiri da abokin takararsa, Benjamin Nathus sun sanar da ficewa daga jam'iyyar a cikin wata wasiƙa da suka ba shugaban LP na Bayelsa
  • Tsohon ɗan takarar gwamnan ya bayyana cewa ya fara neman shawarwar domin zaɓar jam'iyyar da zai koma

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bayelsa - Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar LP a zaɓen da ya gabata a jihar Bayelsa, Udengs Eradiri da abokin takararsa, Benjamin Nathus, sun sanar da ficewa daga jam’iyyar.

Rahotanni sun bayyana cewa galibin shugabannin jam'iyyar a ƙananan hukumomin jihar Bayelsa sun bi sahun Eradiri da Nathus domin ficewa daga LP.

Dan takarar gwamna na LP ya fice daga jam'iyyar a Bayelsa
Udengs Eradiri ya fice daga jam'iyyar LP Hoto: Hon. Udengs Eradiri
Asali: Facebook

Udengs Eradiri ya aika wasiƙar yin murabus ɗinsa daga LP ga shugaban jam’iyyar na jihar a birnin Yenagoa, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Ado Doguwa: 'Dan majalisa ya nemi afuwar APC kan yabon gwamnan PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ɗan takarar gwamna ya fice daga LP?

A cikin wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 8 ga watan Disamba, Eradiri ya ce ya ɗauki matakin ne domin ya samu damar ci gaba da gudanar da harkokinsa na siyasa, a jam'iyyar da ta shirya samar da irin shugabancin da ya dace da Bayelsa.

Eradiri ya yabawa ƴaƴan jam’iyyar LP, waɗanda suka yi amanna da burinsa na ganin Bayelsa ta inganta, suka ba shi damar zama ɗan takarar gwamna.

Eradiri, wanda ya zo na uku a zaɓen gwamnan da ya gabata a jihar, ya ce magoya bayansa sun goyi bayan matakin da ya ɗauka, rahoton Leadership ya tabbatar.

Wace jam'iyyar zai koma?

Tsohon ɗan takarar gwamnan, ya ce yana ci gaba da neman shawarwari domin yanke shawara kan jam'iyyar da zai koma wacce za ta ba shi damar yi wa jama’a hidima.

"Muna ci gaba da shawarwari sosai tare da tuntuɓar duk masu ruwa da tsaki domin sanin jam’iyyar siyasar da za mu koma."

Kara karanta wannan

An yi musayar yawu da wani ɗan Majalisar Tarayya ya sanar da komawa APC

"Jam’iyyar mu ta gaba za ta kasance irin wacce za ta ba mu damar yin hidima ga jama’a da kuma ciyar da jihar Bayelsa gaba."

- Udengs Eradiri

Ɗan majalisa ya fice da LP

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan jam'iyyar LP a majalisar wakilan Najeriya, Hon. Dalyop Chollom ya sauya sheƙa zuwa APC mai mulki.

Hon. Dalyop Challun wanda ke wakiltar mutanen Barkin Ladi/Riyom daga jihat Plateau, ya sanar da barin jam'iyyar LP tare da komawa APC ne a zauren majalisar wakilai da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng