Shugabannin NNPP na Jihohi 6 Sun Yi Magana kan Jagorancin Kwankwaso
- Shugabannin NNPP na jihohi shida sun musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa jam'iyyar ta dare gida biyu saboda rikicin cikin gida
- A wata sanarwa da suka fitar a Fatakwal, sun ce NNPP a dunƙule take karƙashin jagorancin Ajuji Ahmed da jagora Rabiu Kwankwaso
- Sun ce tsagin Agbor Major da sauran ƴan tawagarsa ba ƴan NNPP ba ne domin an jima da korarsu daga jam'iyy mai kayan dadi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Kungiyar shugabannin NNPP na jihohin Kudu ta yi watsi da rahotannin da ake yaɗawa cewa jam'iyya na fama da rigingimun cikin gida.
Ciyamonin NNPP na jihohin Kudu maso Kudu ne suka karyata jita-jitar a wata sanarwa da suka rabawa manema labarai a Fatakwal, jihar Ribas.
Vanguard ta ruwaito cewa sanarwar na ɗauke da sa hannun shugaban NNPP na Akwa Ibom, Inemisit Akpan da takwarorinsa na jihohin Delta, Edo, Bayelsa, Ribas da Kuros Riba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ciyamomin NNPP na tare da Kwankwaso
Ƙungiyar ciyamomin ta kara da cewa raɗe-raɗin da ke yawo cewa rikici ya ɓarke a NNPP ba gaskiya ba ne, wasu makiyan jam'iyyar ne ke neman tada hankali.
Ta ce NNPP na nan a dunkule karkashin shugabancin Dr. Ajuji Ahmed da kuma jagoran jam'iyyar na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, cewar Daily Post.
Shugabannin NNPP sun yi fatali da tsagin Major
A sanarwar, shugabannin NNPP na jihohi shida suka ce:
"Babu wani rikici da ke faruwa a NNPP kuma mutanen da ake ta surutu a kansu Dr. Bonfiace Okechukwu Aniebonam, Dr. Agbo Gilbert Major, Mr. Oginni Olaposi da sauransu ba ƴan jam'iyya ba ne."
"Dukkansu an kore su daga NNPP tun tuni kuma a halin yanzu ba su da ikon bayyana kansu a matsayin ƴan jam'iyya. Muna ƙara jaddada cewa babu wani tsagi a NNPP.
"A dunƙule muke wuri ɗaya karkashin jagorancin Dr. Ajuji Ahmed da sauran ƴan kwamitin gudanarwa watau NWC."
NNPP za ta ba mutane mamaki
Wani ɗan Kwankwasiyya, Mubarak Yusuf ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa jam'iyyar NNPP za ta ba mutane mamaki a zaɓuka masu zuwa.
A cewarsa, sun ɗauki darasi a zaɓen 2023 kuma za su yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen wayar da kan ƴan Najeriya su gane cewa PDP da APC duk abu ɗaya ne.
"Babu wani rikici a NNPP kamar yadda shugabannin kudu suka faɗa, kan mu a haɗe yake karkashin jagoranmu mai girma Kwankwaso.
"Ina tabbatar maka cewa zaɓen 2023 somin taɓi ne, kuma kowa ya gani har kujerar gwamna muka karɓa daga hannun jam'iyya mai mulki.
"Mun ɗauki darasi kuma zaɓuka na gaba ina da yaƙinin za a sha mamakin NNPP," in ji jigon na NNPP.
NNPP ta rasa wasu jiga-jigai a Kano
Kun ji cewa tsohon kansilar mazabar Sanata Rabiu Kwankwaso, Yahaya Sa’idu da wasu jiga-jigan NNPP sun sauya sheka zuwa APC.
Hakazalika, an samu wasu kusoshin jam'iyyar PDP daga karamar hukumar Dawakin Kudu sun koma jam'iyyar APC a Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng