A Karshe, An Fallasa 'Dabarar' da APC Ta Yi Buhari Ya Samu Nasara a Zaben 2015
- Chidi Odinkalu ya ce APC ta samu nasara a 2015 ta hanyar zanga-zanga, sai ga shi yanzu tana murkushe masu zanga zanga
- Tsohon shugaban hukumar NHRC ya ce zanga-zanga hakki ne na al’umma ba na gwamnati ba, amma APC ta take wannan hakkin
- Ya yi bayanin yadda APC ta hau mulki a wani taro na tunawa da 'Ranar Kare Hakkin Dan Adam' da Global Rights ta shirya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Chidi Odinkalu, tsohon shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa (NHRC), ya ce APC mai mulki tana hana zanga-zanga, duk da cewa hakkin al'umma ce.
Odinkalu ya bayyana haka ne a wani taro da Global Rights, wata kungiya mai zaman kanta, ta shirya, mai taken “Zanga-zanga a Najeriya.”
Taron ya gudana a shafin X na @Globalrightsng domin tunawa da ranar kare hakkin dan adam ta duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Najeriya na karkashin masu zanga zanga'
A yayin da ya ke tsokaci, tsohon shugaban hukumar NHRC ya yi ikirarin cewa APC ta yi amfani da zanga zanga ta samu nasara a zaben 2015.
Chidi Odinkalu ya ce:
“Zanga-zanga hakki ne na al’umma. A karkashin doka, ana sanar da gwamnati domin ta kare masu zanga-zangar da dukiyarsu.”
“A yanzu, Najeriya tana karkashin mulkin wadanda suka yi fice wajen yin zanga-zanga, daga shugaban kasa har zuwa wasu mukarraban gwamnatinsa.”
Yadda APC ta yi nasara a zaben 2015
Tsohon shugaban hukumar ta NHRC ya ci gaba da cewa:
“APC ta samu nasarar siyasa a 2015 ta hanyar zanga-zanga da ya hada jam'iyyar APC, don samun goyon bayan jama’a wajen karbe mulki.”
“Zanga-zanga a baya tana da tasiri kuma ana girmama ta sosai, duk da cewa akwai kalubale. Amma tun bayan hawa mulki, sun danne wannan hakki.”
“Misali shi ne zanga zangar 'BringBackOurGirls' da suka jagoranta a baya, sun yi amfani da ita wajen samun soyayyar mutane, amma da suka hau mulki, suka rufe babin."
APC ta dauki matakin hana zanga zanga
A wani labarin, mun ruwaito cewa Abdullahi Umar Ganduje ya gana da shugabannin APC na jihohi domin duba hanyar dakile zanga zangar da shirya yi a Agusta.
Yayin da shugaban APC na kasa ya nuna damuwa kan zanga zangar adawa da gwamnatin Bola Tinubu, ya roki matasa a lokacin da su hakura da fitowa zanga zangar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng