Ana Batun Tazarcensa, Shugaba Bola Tinubu Ya Aika Sako ga 'Yan Adawa

Ana Batun Tazarcensa, Shugaba Bola Tinubu Ya Aika Sako ga 'Yan Adawa

  • Mai girma Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna muhimmancin da zaman lafiya da haɗin kai suke da shi
  • Bola Tinubu ya buƙaci ƴan adawa da su rungumi zaman lafiya domin ƴan Najeriya abu ɗaya ne duk da bambancin da suke da shi a siyasa
  • Kalaman na shugaban ƙasan na zuwa ne bayan sakataren gwamnatin tarayya ya nuna cewa ya kamata ya zarce a shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ƴan adawa da su rungumi zaman lafiya da haɗin kai.

Shugaba Bola Tinubu ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

Tinubu ya aika sako ga 'yan adawa
Tinubu ya bukaci a zauna lafiya Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Bola Tinubu ya ba ƴan adawa shawara

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa duk da cewa akwai bambancin siyasa, ƴan Najeriya ƴan gida ɗaya ne, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

'Abin da ya kamata Atiku da Peter Obi su yi don kayar da APC a zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata a hedkwatar hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS) da ke birnin tarayya Abuja.

Tinubu ya ƙaddamar da aiki a hedkwatar NIS

Tinubu ya je hedkwatar hukumar ne domin ƙaddamar da cibiyar fasaha ta 'Bola Ahmed Tinubu Technology Innovation Complex' (BATTIC).

Ya bayyana cewa ƴan Najeriya ƴan gida ɗaya ne waɗanda suke zaune a cikin ɗakuna daban-daban.

Tinubu dai ya isa hedkwatar hukumar NIS ne a Abuja da misalin ƙarfe 12:08 na rana domin ƙaddamar da BATTIC.

Ya samu tarba daga ministan harkokin cikin gida, Olabunmi Tunji-Ojo da shugabar hukumar shige sa fice ta ƙasa, Kemi Nandap.

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, shugabannin hukumomi da dai sauransu, sun halarci bikin.

Atiku ya yi martani kan hakura da takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Alhaji Atiku Abubakar ya yi wa sakataren gwamnatin tarayya martani kan kiran da ya yi masa na haƙura da takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Atiku ya maida martani bayan Akume ya bukaci ya hakura da takara

Tsohon ɗan takarar na PDP a zaɓen 2023, ya bayyana cewa ƴan Najeriya ne suke da ikon zaɓar wanda suke so ya jagorance su idan lokacin ya yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng