Zaben 2027: Atiku Ya Maida Martani bayan Akume Ya Bukaci Ya Hakura da Takara

Zaben 2027: Atiku Ya Maida Martani bayan Akume Ya Bukaci Ya Hakura da Takara

  • Atiku Abubakar ya yi martani ga sakataren gwamnatin tarayya kan buƙatar ya haƙura da neman shugabancin Najeriya a 2027
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya tunatar da George Akume cewa yankin Kudu ya fi na Arewa daɗewa kan mulkin Najeriya
  • Atiku ya kuma nuna cewa ƴan Najeriya ne ke da ikon zaɓar wanda suke son ya hau kan kujerar mulkin ƙasar nan idan an shiga zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa akwai bambancin shekara shida na tsawon lokacin da Arewa da Kudu suka shafe a kan shugabancin ƙasar nan.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake maida martani ga kiran da Sanata George Akume, ya yi ga masu son shugabancin Najeriya daga Arewa su jira har sai 2031.

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban kasa ya yabi Tinubu ana batun kudirin haraji

Atiku ya yi wa George Akume martani
Atiku ya yi wa sakataren gwamnatin tarayya martani Hoto: @OfficialAzzaki, @SGFAkume
Asali: Twitter

'Kudu ta fi Arewa daɗewa a mulki', Atiku

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya maida martanin ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe ya fitar, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya bayyana cewa nan da shekarar 2027, yankin Kudu zai yi shekara 17 yana shugabancin Najeriya, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Idan ba a manta ba dai, Akume ya buƙaci ƴan Arewa da ke shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 da su ajiye burinsu su jira har zuwa 2031, lokacin da shugaba Bola Tinubu ya kammala wa'adinsa na biyu.

Wane martani Atiku ya yi wa Akume

Sai dai, Atiku ya ce yankin Kudu ya fi na Arewa daɗewa kan shugabancin ƙasar nan tun bayan dawowa mulkin dimokuraɗiyya.

"To, a ina gaskiya da adalci suke? A shekarar 2027, yankin Kudu ya yi mulkin shekara 17, shekara takwas a ƙarƙashin Obasanjo, shekara biyar a ƙarƙashin Jonathan da shekara huɗu a ƙarƙashin Tinubu."

Kara karanta wannan

"Ba mu son kowa ya kwana da yunwa," Shugaba Tinubu ya shirya wadata abinci a Najeriya

"Yayin da yankin Arewa ya yi shekara 11 kawai, Yar'Adua ya yi shekara uku sai Buhari ya yi takwas."
"Wannan ya samar da bambanci na tsawon shekara shida a tsakanin Arewa da Kudu, lamarin da ya haifar da rashin raba daidai kan mulki."
"A kowane hali dai, ikon zaɓe da zaɓar gwamnati ya ta’allaka ne ga al’ummar Najeriya, da aka ba su amana, da kuma ƙoƙarin gwamnati na maida kanta matsayin wacce ta cancanci samun ƙuri'un jama'a."
"Amma shin gwamnatin Tinubu ta nuna cewa ta cancanci a sake zaɓar ta? Sai dai, kash amsar hakan a bayyane take ƙarara, Allah ya kiyaye."

- Atiku Abubakar

Atiku Abubakar ya caccaki ƴan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar, ya caccaki ƴa sandan Najeriya kan yadda suka cafke mai fafutukar kare hakkin dan Adam a Legas.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ce bai dace ƴan sanda su rika wuce gona da iri ba a wajen amfani da ikon da kasa ta ba su saboda tsirarun mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng