'Wasu Ƙarin Yan Majalisar Tarayya na Shirin Komawa Jam'iyyar APC Mai Mulki'

'Wasu Ƙarin Yan Majalisar Tarayya na Shirin Komawa Jam'iyyar APC Mai Mulki'

  • Mamban Majalisar wakilai, Hon. Etanabene Benedict ya ce yana ganin har yanzu akwai ƴan majalisar LP da ka iya komawa APC
  • Ɗan Majalisar wanda ya fito daga jihar Delta ya ce abokan aikinsa na LP na komawa APC ne da nufin samun tikitin dawowa majalisa a 2027
  • A ranar Alhamis da ta wuce ne ƴan majalisa hudu suka sanar da ficewa daga LP zuwa APC mai mulki a zauren majalisar wakilai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ɗan majalisar wakilan tarayya na LP, Hon. Etanabene Benedict ya ce galibin takwarorinsa na jam'iyyar sun fara duba yiwuwar sauya sheka zuwa APC.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa mambobin na ƙoƙarin komawa APC ne a wani ɓangare na shirye-shiryen yadda za su sake dawowa majalisa a zaɓen 2027.

Majalisar wakilai.
Etanabene Benedict ya ce akwai sauran ƴan majalisar LP da za su koma APC nan gaba Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Benedict ya yi wannan furucin ne a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels raar Juma'a.

Kara karanta wannan

Bayan sauya sheƙar diyar tsohon gwamna, PDP ta kori ɗan Majalisar Tarayya nan take

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan Majalisar tarayya 4 sun koma APC

A ranar Alhamis da ta gabata, wasu mambobin jam’iyyar LP hudu a majalisar wakilai suka sanar da komawa jam’iyyar APC a hukumance.

‘Yan majalisar dai sun bayyana rikicin cikin gida da ya addabi LP musamman a matakin ƙasa a matsayin dalilinsu na barin jam'iyyar zuwa APC.

Jam'iyyar LP ta yi magana kan lamarin

LP ta nuna rashin jin daɗi game da sauya shekar, tana mai cewa za ta ɗauki matakin shari'a a kan 'yan majalisar.

Jam’iyyar LP ta ce za ta nemi kakakin majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas da ya bayyana kujerun ‘yan majalisar a matsayin waɗanɗa ba kowa.

Amma Hon. Benedict, wanda ke wakiltar mazabar Okpe/Sapele/Uvwie a Delta, ya ce ‘yan majalisar sun koma APC ne a matsayin dabarar tunkarar zaɓen 2027.

Wasu ƙarin ƴan LP na shirin shiga APC

"Suna mantawa ne idan aka zaɓe ka a wani muƙami akwai wa'adin, idan ya kare, mutane ke da wuƙa da nama a ko wace jam'iyya kake, idan sun ga dama su kara zaɓenka, idan ba su dama ba su canza."

Kara karanta wannan

'Babban dalilin da ya sa ƴan Majalisar Tarayya 4 suka sauya sheka zuwa APC'

Har yanzu akwai wasu da yawa a cikin jam'iyyar LP da suke tunani irin wannan watau su koma APC. Don haka, idan ya faru gobe, ba zan yi mamaki ba."

- Hon. Etanabene Benedict.

An yi hayaniya a Majalisar Wakilai

A wani labarin, an ji cewa wata ƴar hayaniya ta ɓarke a zauren Majalisar wakilai kan kudirin haraji da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya gabatar.

Lamarin ya fara ne lokacin da wani ɗan majalisa ya furta cewa su ne suka fara goyon bayan kudirin harajin Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262