Ribas: Gwamna Ya Tuna Abin da Ƴan Sanda Suka Yi, Ya Faɗi Sarakuna 2 da Aka 'Wulaƙanta'
- Gwamna Fubara na jihar Ribas ya yabawa sarakuna biyu da suka fuskanci cin mutunci saboda goyon bayan gwamnatinsa
- Sir Siminalayi Fubara ya ce gwamnatinsa ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen inganta rayuwar al'umma a jihar Ribas
- An naɗa gwamnan sarautar gargajiya a wurin taron buɗe makarantar sakandiren gwamnati ta mata a garin Ahoada, ƙaramar hukumar Ahoada ta Gabas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya ce ba zai yi ƙasa a guiwa ba wajen zuba ayyukan da za su inganta rayuwar al'ummarsa.
Gwamnan ya nanata waɗannan kalamai ne a taron bikin buɗe makarantar sakandiren gwamnati ta mata da ya sabunta a garin Ahoada ranar Juma'a.
An naɗawa gwamna rawanin sarauta
Punch ta ce a wurin taron an ba gwamnan sarautar Eze Yawe Ugo na ƙasar Ekpeye watau ma'ana sarkin nishaɗin ƙasar Ekpeye.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya bayyana cewa ya gaji aikin makarantar ne a lokacin da ya karbi ragamar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2024.
A cewarsa, duk da gadar aikin yayi amma ya yanke shawarar ci gaba da aiki da ‘yan kwangila uku da aka ba aikin saboda batun ilimi na fifiƙo na musamman a gwamnatinsa.
Gwamna Fubara ya nuna godiya ga mutanen Ekpeye bisa goyon bayan da suke bai wa gwamnatinsa duk da suna fuskantar tsangwama da cin zarafi.
Gwamna Fubara ya yabi sarakuna 2
Ya yi ikirarin cewa an ci mutuncin wasu daga cikin sarakunan su kamar, Eze Ekpeye Logbo, Mai Martaba Eze Kelvin Anugwo, da Eze Cassidy Ikegbidi kuma aka kama su.
Fubara ya ce:
“Lokacin da Eze Ekpeye ke magana, da yawa daga cikinku ba ku fahimci abin da ya faru ba. Saboda goyon bayan da suka ba ni, an kama shi, an tuhume shi kan zargin karya.
"Ya zauna a hannun ‘yan sanda sama da watanni hudu; shi da Cassidy."
Gwamnan ya yi alkawarin cika rokon da Eze Ekpeye Logbo da wasu sarakuna suka yi na ƙara wasu kujerun sarautar gargajiya a yankin.
Jonathan ya yabawa Gwamna Fubara
A wani rahoton kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya jinjinawa Gwamna Fubara kan yadda yake iya ɗaukar dambarwar siyasar Ribas.
Jonathan ya ce gwamnan ya maida hankali kan kawo ci gaba da Ribas da yankin Neja Deƙta gaba ɗaya duk da matsalolin da yake fuskanta.
Asali: Legit.ng