"Ƴan Kwankwasiyya ba Su Son Zaman Lafiya," An Kori Kwankwaso da Mabiyansa daga NNPP
- Tsagin NNPP a ƙarƙashin jagorancin Agbu Major ya tabbatar da cewa Rabiu Kwankwaso da mabiyansa ba ƴan jam'iyya ba ne
- Major ya ce korar da jam'iyyar NNPP ta yi wa ƴan Kwankwasiyya na nan daram kuma kotu ta tabbatar da hakan kwanan nan
- A cewar 'dan siyasar, ƴan Kwankwasiyya wasu mutane ne da ba su kaunar zaman lafiya kuma ba su bin doka sau da ƙafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsagin jam'iyyar NNPP ya kara jaddada cewa matakin korar ɗan takarar shugaban ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso da mabiyansa na nan daram.
Shugaban tsagin na ƙasa, Agbu Major ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai ranar Juma'a a birnin Abuja.
Ya ce NNPP ƙarƙashin jagorancinsa ta kori Kwankwaso da mabiyansa ƴan Kwankwasiyya daga jam'iyyar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsagin NNPP ya gargaɗi Rabiu Kwankwaso
Major ya gargadi Kwankwaso da tawagarsa ta ƴan Kwankwasiyya su guji yi wa jam'iyyar zagon ƙasa da kuma yin duk wani abu da zai ruguza NNPP.
A cewarsa, a ƴan kwanakin nan tsagin Kwankwaso ya nemi maye gurbin mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, Ali Madaki da wani daban.
"Duk da cewa su ba ƴan NNPP ba ne, sun ci gaba da ƙoƙarin kawo tangarda ga ƴan jam'iyya a majalisar dokoki ta ƙasa," in ji Agbu Major.
Jam'iyyar NNPP ta aika sako ga hukumomin tsaro
Major ya yi kira ga hukumomin tsaro musamman na jihar Kano da su yi bincike tare da dakile duk wani abu na ƙokarin tada zaune tsaye da Kwankwasiyya ke yi.
Shugaban NNPP ya ce:
"Wannan tawaga ta Kwankwasiyya kowa ya san su da rashin son zaman lafiya, rashin hankali da neman faɗa, don haka muna kira ga jami'an tsaro su tabbatar da bin doka da oda."
"Akwai bukatar jami'an tsaro su tashi tsaye su tabbatar da bin doka da oda a Kano duba da hukuncin da kotu ta yanke na tabbatar da korar Kwankwaso da mabiyansa."
Wani jigon NNPP, Saidu Abdullahi ya shaidawa Legit Hausa cewa waɗannan mutanen neman a sansu kawai suke yi shiyasa suke taba Kwankwaso.
Ɗan Kwankwasiyyar ya ce Madugu shi ne NNPP domin idan yau ya sanar da barin jam'iyyar babu wanda zai sake zama.
Malam Saidu ya ce:
"Kamar yadda na taɓa faɗa maka a baya, waɗannan mutanen ƴan neman suna ne, idan ka kori Kwankwaso to kuma wa ya rage a NNPP? Saboda haka haushi kawai suke kuma na san mai gida ba zai tanka ba."
Jigon NNPP a Kudu ya fice daga jam'iyyar
A wani labarin, kun ji cewa Alhaji Adebisi Olopoeyan wanda jagoran NNPP ne a yankin Kudu maso Yamma ya sanar da fucewarsa daga jam'iyyar.
Tsohon jigon na NNPP ya bayyana cewa ya yi murabus daga jam'iyyar ne bisa wasu dalilai na ƙashin kansa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng