Tsohon 'Dan Takarar Gwamna da Magoya Bayansa Sun Fice daga Jam'iyyar LP
- Yayin da LP ke shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027, tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Edo ya fice daga jam'iyyar
- Kenneth Imansuangbon ya tabbatar da barin LP a wata wasiƙa da ya aikewa shugaban jam'iyyar na ƙasa, Julius Abure
- Ya ce rigingimin cikin gida na ɗaya daga cikin dalilin da suka sa ya tattara magoya bayansa suka fice daga LP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Tsohon ɗan takarar gwamna na jam'iyyar LP a jihar Edo, Kenneth Imansuangbon ya fice daga jam'iyyar.
Kenneth Imansuangbon ya tabbatar da haka ne a wata takarda da ya aika wa shugaban LP na ƙasa, Julius Abure da shugaban jam'iyya na gundumarsa a Ewohimi.
Premium Times ta kawo cewa Mista Imansuangbon ya sha kaye a zaben fitar da ɗan takarar gwamnan LP a hannun tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi, Olumide Akpata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma bayan haka, jam'iyyar LP ta ƙare a matsayi na uku a yawan ƙuri'u a zaɓen gwamnan jihar Edo da aka yi ranar 16 ga watan Nuwamba.
Dalilin tsohon ɗan takarar gwamna na barin LP
Mista Imansuangbon ya bayyana rashin tsari a cikin gida da rikicin shugabanci da ya dabaibaye LP a matsayin dalilansa na ficewa daga jam'iyyar.
A cewarsa, jam’iyyar LP ta kauce daga kan turbar da aka kafa ta a kai, wanda hakan ya sanya ta gaza zama zaɓin da ‘yan Nijeriya ke so, rahoton Punch.
Jigon siyasar ya zargi shugabannin LP da maida jam'iyyar tamkar wani dandalin kasuwanci, wanda ya sa ta kauce daga manufarta na ƙarfafa guiwar jama'a.
Imansuangbon ya dauke mabiyansa daga LP
"Bayan tuntubar magoya bayana a fadin jihar Edo, na ga ya zama dole ni da mabiyana mu fice daga jam'iyyar LP," in ji shi.
Wanda ake yi wa lakabi da “Mutumin shinkafa” saboda rabon shinkafa kyauta a duk shekara a fadin Edo, ɗan siyasar ya taba zama a APC da kuma PDP a baya.
Ɗan takarar jam'iyyar LP ya rungumi kaddara
A wani labarin, an ji cewa bayan zaben gwamnan Edo, ɗan takarar LP ya sanar da cewa ba zai ƙalubalanci nasarar da APC ta samu a gaban kotu ba.
Olumide Akpata ya ce ya dauki wannan matakin ne bayan tattaunawa mai zurfi da tawagar lauyoyinsa da kuma masu ruwa da tsaki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng