An Nemi Ministan Tinubu Ya Yi Murabus, Ya Sake Neman Takarar Gwamna

An Nemi Ministan Tinubu Ya Yi Murabus, Ya Sake Neman Takarar Gwamna

  • Magoya baya sun fara rokon ministan harkokin arzikin ruwa, Adegboyega Oyetola ya dawo ya sake neman takarar gwamna
  • Kungiyar IPSC ta magoya bayan APC ta bukaci Oyetola ya sake dawowa bayan kayen da ya sha a zaɓen da ya gabata a Osun
  • A cewar kunguyar, shi kaɗai ne zai nemi takara a zauna lafiya a jam'iyyar APC reshen jihar Osun saboda shi ne jagora

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun - Yayin da ake tunkarar zaben gwamnan jihar Osun a 2029, an fara kiraye-kirayen ga tsohon gwamna, Adegboyega Oyetola ya dawo ya sake tsayawa takara.

Oyetola wanda a yanzu shi ne ministan kula da harkokin tattalin arzikin ruwa a gwamnatin Bola Tinubu ya sha kaye a zaɓen da aka yi a shekarar 2022.

Adegboyega Oyetola.
Kungiyar ta buƙaci tsohon gwamnan Osun, Oyetola ya sake neman takara a zaben 2026 Hoto: Adegboyega Oyetola
Asali: Twitter

Kungiya ta nemi minista ya dawo Osun

Kara karanta wannan

Shugaban karamar hukuma zai fara biyan zawarawa alawus duk wata a Najeriya

The Nation ta ruwaito cewa kungiyar magoya bayan APC (IPSC) ta buƙaci Oyetola ya aje kujerar minista, ya sake neman zama gwamnan Osun a 2026

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar, Dr. Adeyoola Adejare da sakatare, Adekanmi Adelana sune suka roki Oyetola ya dawo a wani taron manema labarai a Osogbo.

Sun bayyana tasirin da ministan ke da shi wajen haɗa kan ƴa ƴan jam'iyyar APC a jihar da kuma nagartarsa a shugabanci, rahoton Punch.

Dalilin rokon Oyetola ya tsaya takarar gwamna

"Gogewar Oyetola a wajen tafiyar da harkokin kudi cikin gaskiya da riƙon amana da tsare-tsare masu kyau kaɗai za su ba shi nasara a zaɓen gwamnan Osun na 2026," in ji Adejare.
"Idan kuma ya ki yarda ya sake neman takara, haka zai ba ƴan siyasa ƙofar nuna sha'awarsu, wanda ka iya kawo rigima da rarrabuwar kai a jam'iyyar APC.
"Amma idan ya amsa kira ya sake dawowa ya tsaya takara babu wanda zai ce uffan saboda dama shi ne jagoran jam'iyyar a Osun," in ji Adejare.

Kara karanta wannan

NLC ta janye yajin aiki, gwamna ya amince N80,000 ya zama mafi ƙarancin albashi

NNPP ta hango nasara a zaɓen gwamnan Osun

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta ce tana ganin cinta a zsɓen gwamnan jihar Osun mai zuwa a 2026.

NNPP ta ce wahalhalin da ake ciki za kashewa APC kasuwa yayin da ita kuma PDP ta gaza cika alkawurran da ta ɗaukarea mutanen Osun.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262