"Najeriya na Bukatar Mace Ta Zama Shugaban Kasa," Babban Sarki Ya Yi Bayani
- Obi na Onitsha, Mai martaba Alfred Achebe ya ce lokaci ya yi da Najeriya za ta bari mace ta zama shugaban kasa
- Basaraken ya bayyana cewa yana ganin mace za ta iya kawo sauyin da ƴan Najeriya suka daɗe suna nema a ƙasar nan
- Sarkin ya kafa misali da gwamna mace da aka taɓa yi a Anambra da kuma firaminista biyu mata da aka yi a Burtaniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Yayin da ake tunkarar babban zabe a 2027, Obi na Onitsha, Mai Martaba Alfred Achebe ya ce Najeriya na bukatar a samu mace ta zama shugaban ƙasa.
Sarkin ya kafa misali da yadda ƙasar Burtaniya ta yi firaminista mata har guda uku a tarihi.
'Najeriya na bukatar mata su karɓi mulki'
Basaraken ya bayyana kwarin guiwar cewa shugabar ƙasa mace za ta yi aiki na ban mamaki kuma ta jawo sauyi a Najeriya, kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obi na Onitcha ya yi wannan furuci ne a taron kaddamar da littafin tarihin Sanata Chris Anyanwu mai suna 'Bold Leap'.
An gudanar da bikin kaddamarwar ne dakin taro na hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) da ke babban birnin tarayya na Abuja.
Sarkin ya kuma bayar da misali da Dame Virginia Etiaba, mace ta farko da ta zama gwamna a Najeriya, cewar rahoton Daily Post.
Etiaba ta zama gwamnan jihar Anambra daga watan Nuwamba 2006 zuwa Fabrairu 2007.
Sarkin ya ba da misali da jihar Anambra
"Jihar Anambra ta yi gwamna mace, Dame Etiaba, don haka idan muna son kawo sauyi a rayuwar da muke ciki muna mmbukatar mata kamar Chris Anyanwu.
"A Najeriya muna da surutu a baki, ina ganin lokaci ya yi da za mu fara yin wani abu daban. Mu na da zaɓi guda biyu, ko dai mu cigaba da shayar da saniya har ta mutu saboda son rai, muna hawa mulki ba don al'umma ba.
"Ko dai mu cigaba da hakan ko kuma mu koma ɗaya ɓangaren mu ɗaga Najeriya zuwa mataki mai kima da daraja."
- Mai martaba Alfred Achebe.
LP ta fara shirin tunkarar zaben 2027
A wani rahoton, kun ji cewa jam’iyyar LP ta fara shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027 wanda take sa ran karɓe mulkin Najeriya.
LP wacce na ɗaya daga cikin manyan jam'iyyun adawa za ta kafa kwamitocin shugabanci a jihohin Najeriya 36 domin ƙulla alaƙa da al'umma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng