Jam'iyyar NNPP Ta Hango Kujerar Gwamnan da Za Ta Iya Ƙwacewa daga Hannun PDP

Jam'iyyar NNPP Ta Hango Kujerar Gwamnan da Za Ta Iya Ƙwacewa daga Hannun PDP

  • Jam'iyyar NNPP ta bayyana ƙwarin guiwar cewa za ta kai labari a zaɓen gwamnan jihar Osun da za a yi a shekarar 2026
  • NPPP ta ce Gwamna Adelmola Adeleke ya gaza kuma tanq da yaƙinin mutanen Osun za su yi kokarin canza shi a zaɓe mai zuwa
  • Sai dai jam'iyyar PDP ta mayar da martani ga NNPP, inda ta ce nasarorin mai girma gwamna za su ba shi damar tazarce a 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Jam'iyyar NNPP reshen jihar Osun ta lashi takobin kwace mulkin jihar daga hannun Gwamna Ademola Adeleke a zaben gwamnan da za a yi a 2026.

NNPP ta bayyana aniyarta ne a wurin taron kaddamar da ofisoshinta a kananan hukumomin Ila, Boripe, da Ifelodun a ranar Alhamis da ta wuce.

Kara karanta wannan

CBN ya shirya share hawayen ƴan Najeriya, ya taso bankuna kan takardun Naira

Gwamna Ademola Adeleke.
An fara musayar yawu tsakanin NNPP da PDP kan tazarcen gwamnan Osun a 2026 Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Twitter

NNPP ta hango nasara a zaɓen Osun

Da yake jawabi a wurin taron a Ila, shugaban NNPP na Osun, Dr. Tosin Odeyemi, ya bayyana kwarin guiwar cewa jam’iyyar za ta bada mamaki a zabe na gaba, Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, yadda mutane suka dawo daga rakiyar gwamnatin Adeleke da halin matsin da ake ciki a kasa za su taimakawa NNPP wajen samun galaba.

"Muna da damar lashe zaɓen gwamnan Osun a 2029, NNPP ta ƙara yaɗuwa tun kafuwarta.
"Matsin tattalin arziki da ake fama da shi ne zai kashe kasuwar APC, a nan kuma PDP ta gaza. Wannan wata dama ce da za mu kawo ƙarshen mulkin Adeleke," in ji Odeyemi.

PDP ta mayar da martani ga NNPP

Sai dai waɗannan kalamai ba su yi wa jam'iyyar PDP daɗi ba, inda ta bayyana ikirarin NNPP da soki burutsu.

Jam'iyyar PDP ta jaddada cewa nasarorin da Gwamna Ademola Adeleke ya samu kaɗai sun isa su sa al'ummar Osun su sake zaɓensa karo na biyu.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa ban miƙawa Ganduje shaidar cin zaɓena ba," Gwamnan Ondo ya kare kansa

Daraktan yada labarai na PDP a jihar Osun, Oladele Bamiji, ya ce:

“Maganar da NNPP ta yi ba ta da tushe balle makama, burinsu kawai su faranta wa masu daukar nauyinsu rai, ba za su iya hana Gwamna Adeleke tazarce a 2026 ba."

Jam'iyyar NNPP ta caccaki Ganduje

A wani rahoton, an ji cewa kalaman da Abdullahi Umar Ganduje ya yi na APC na shirin ƙwace jihohin Osun da Oyo a zaɓe mai zuwa ba su yi wa shugaban NNPP daɗi ba

Shugaban NNPP na jihar Osun ya ja kunnen Abdullahi Umar Ganduje da ya guji yin kalaman da za su tada fitina a yankin Kudu maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262