Kwadayi Mabudin Wahala: APC Ta Ki Karbar Yan PDP da Suka Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar
- Wasu yan jam'iyyar PDP sun ga ta kansu yayin aka ki karbarsu a APC bayan sun sauya sheka a jihar Ondo da ke Kudancin Najeriya
- Lamarin ya faru ne a gundumar Ogbagi da ke Akoko inda shugabannin jam'iyyar suka ce ba za su amince da su ba a cikin APC
- Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi nasarar lashe zaben gwamnan jihar da aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - wasu mambobin jam’iyyar APC a jihar Ondo sun ki amincewa da yan PDP da suka sauya sheka.
Yan APC da ke mazabar Ogbagi a Akoko sun yi watsi da mambobin PDP ne kan abin da suka ce bai halatta ba.
Ana zargin PDP dakai hare-hare a Ondo
The Nation ta ruwaito cewa wadanda suka sauya sheka daga PDP sun samu jagorancin Bobade Gboyega, wanda aka fi sani da “Danger.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan bai rasa nasaba da hare-haren da ake zargin wadanda suka sauya shekar suka yi a yankin Awe.
Wasu na zargin yan PDP sun sauya sheka ne domin tsira daga hukunci inda wani hadimin Gwamna ya ce ba zai yiwu ba dole a dauki mataki.
An ki karbar yan PDP da suka koma APC
Yan jam'iyyar a yankin bayyana karɓar waɗannan mutane daga PDP da wasu shugabannin APC na yankin suka yi a matsayin abin da ba za a yarda da shi ba saboda rashin inganci.
Yan APC a Ogbagi suka ce an yaudare su wurin karbar Bobade a matsayin dan jam'iyyar inda suka ce ba za su taba amincewa da shi ba.
Fusatattun yan APC sun bayyana haka ne yayin ziyarar aiki da Hon. Bode Obanla wanda hadimi ne ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya kawo yankin.
Tsohon Minista ya yi murabus daga PDP
Kun ji cewa jam'iyyar PDP a Najeriya ta rasa jigonta yayin da take fama da rikicin cikin gida wanda ya ki ci ya ki cinyewa.
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Osita Chidoka ya yi murabus daga jam'iyyar gaba daya domin sauya wani layi.
Osita ya tabbatar da haka ne a jiya Juma'a 29 ga watan Nuwambar 2024 inda ya mika takardar murabus dinsa a gundumarsa da ke Anambra.
Asali: Legit.ng