Rikicin APC: Kotu Ta Fatattaki Shugabannin da Ganduje Ya Naɗa

Rikicin APC: Kotu Ta Fatattaki Shugabannin da Ganduje Ya Naɗa

  • Rikicin APC ya kara ƙamari a jihar Benue yayin da wata kotu ta fatattaki shugabannin riko da Abdullahi Ganduje ya naɗa
  • A ranar 21 ga watan Agusta shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa shugabannin saboda rikicin siyasa da jam'iyyar ke fama da shi
  • A dalilin haka, shugaban da aka dakatar ya shigar kara gaban kotu domin kalubalantar hukuncin da Abdullahi Ganduje ya yi a watan Agusta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Rikicin APC a jihar Benue ya kara ɗaukar sabon salo yayin da kotu ta fatattaki shugabannin riko.

Austin Agada ne ke ikirarin jagorantar jam'iyyar APC a Benue kafin Abdullahi Ganduje ya kafa kwamitin rikon.

Ganduje
Kotu ta rusa shugabannin APC a Benue. Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mai shari'a Tertsea Kume ya rusa kwamitin riƙon bisa laifin karya doka wajen kafa shi.

Kara karanta wannan

Gasar Alkur'ani: Khadimul Islam, Ganduje ya raba kujerun Hajji da motoci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fatattaki shugabannin APC a Benue

Shugaban APC da aka dakatar a jihar Benue, Austin Agada ya shigar da uwar jam'iyyar kara a gaban kotu.

A ranar Alhamis, mai shari'a Tertsea Kume ya saurari karar kuma ya rusa hukuncin da APC ta yi na kafa kwamitin riko a jihar Benue.

Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ne ya kafa kwamitin a ranar 21 ga Agusta domin su yi wata shida kafin a samu damar magance rikicin jam'iyyar.

"Ko Ubangiji da ya halicci sama sa kasa, ya ba mutane mulki a duniya, idan aka masa laifi yana sauraron mutane.
Da Annabi Adamu ya ci dan itace a Aljanna, ba a kore shi a cikinta ba sai da aka tambaye shi dalili.
Amma uwar jam'iyyar APC ta ƙi sauraron shugaban da ta dakatar, sai ta rusa shugabancinsa ba bisa ka'ida ba."

- Mai shari'a Tertsea Kume

Bayan rusa kwamitin da Ganduje ya naɗa, alkalin kotun ya ce duk hukuncin da yan kwamitin suka yi ma ya rushe.

Kara karanta wannan

Yakubu Gowon: Abin da yake ci mani tuwo a kwarya game da matsalar Arewa

Vanguard ta ruwaito cewa shugaban kwamitin da aka rusa, Benjamin Omale ya ce za su daukaka kara.

Rikicin APC ya shafi sarauta a Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa rikicin cikin gida da ya ɓarke a APC reshen jihar Sakkwato ya fara raba kawunan manyan jiga-jigai da sarakuna.

An ruwaito cewa hakimin Sabon Birni, Alhaji Abdullahi Muhammad Bawa ya yi murabus daga sarauta saboda barin tsagin Sanata Wamakko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng