Edo: Gwamna Ya Taso Hadiman Magabacinsa a Gaba, An Kwato Motoci 30
- Gwamnatin jihar Edo karkashin Gwamna Monday Okpebholo ta kwato motoci 30 daga hannun jami'an tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe
- Shugaban kwamitin karbo motocin wanda gwamna ya kafa, Kelly Okungbowa ne ya tabbatar da hakan ranar Alhamis
- Ya ba nutanen Edo tabbacin cewa kafin cikar wa'adin makonni biyu da aka ba su, za su ƙwato motocin da aka yi sama da faɗi da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Kwamitin kwato motoci na jihar Edo ya karɓo guda 30 daga hannun jami’an gwamnatin da ta shude karkashin Godwin Obaseki.
Shugaban kwamitin wanda Gwamna Monday Okpebholo ya kafa, Kelly Okungbowa shi ne ya tabbatar da ƙwato motoci 30 zuwa yanzu.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran gwamna, Fred Itua, ya fitar yau Alhamis, 28 ga watan Nuwamba, 2024, Punch ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Edo ta ƙwato motoci 30
Mista Okungbowa ya yabawa masu fallasa bayanai waɗanda suka taimaka da sahihan bayanai wajen kwato wasu daga cikin motocin.
Ya ce kwamitin ya ɗauko motoci huɗu daga gidan wani babban hadimi a gwamnatin Obaseki da wata guda ɗaya daga gidan wani daban.
"Mun kwato motoci kirar Land Cruiser guda biyu da Toyota Hilux guda biyu daga hannun wani tsohon babban jami’in gwamnatin da ta shude. Ɗaya daga ciki na ɗauke da fastocin kamfe.
"Mun kuma gano wata motar kirar Hilux, wanda ya sa adadin motocin da aka kwato tun lokacin da muka fara aikin ya kai 30,” in ji Okungbowa.
Kwamitin ya shirya karɓo ƙarin motoci
Ya tabbatarwa al'ummar jihar Ondo cewa nan ba da daɗewa za su kara ƙwato motocin gabanin wa'adin makonni biyu da aka kwamitin ya cika.
Okungbowa ya jaddada cewa kwamitin a shirye yake ya je ko ina a faɗin kasar nan domin kwato motocin gwamnatin Edo a duk inda aka same su.
Idan ba ku manta ba kwamitin ya kwato motoci uku a ranar Juma’ar da ta gabata, mota kirar Hilux daya da motocin bas Toyota Hiace guda biyuz rahoton Daily Trust.
Gwamnan Edo ya samar da motoci kyauta
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Edo ta samar da bas kyauta a fadin jihar domin yin zirga-zirgar al'ummarsa a kyauta.
Monday Okpebholo shi ya amince da hakan domin saukakawa al'umma duba da halin kunci da ake ciki saboda tashin kudin fetur.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng