Mutumin Gombe da Ya Niƙi Gari Ya Tafi Abuja a Keke Ya Samu Kyautar Mota da Kudi
- Ɗan jihar Gombe, Shamsuddeen Garba wanda ya tashi daga gida zuwa Abuja a kan keke ya samu kyautattuka masu gwabi
- Shamsudeen wanda aka fi sani da Ɗan Small ya yi wannan tafiya ne domin nuna goyon baya ga mataimakin ma'ajiyin APC na ƙasa, Dattuwa Ali Kumo
- Dattuwa ya ba Ɗan Small kyautar mota kirar Honda da kuma kudi Naira 700,000 domin yaba masa bisa nuna masa ƙauna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Mutumin nan ɗan jihar Gombe da ke Arewa maso Gabas, Shamsuddeen Garba, wanda ya taso a keke ya isa babban birnin tarayya Abuja.
Mutumin wanda aka fi sani da Ɗan Small ya samu kyautar mota ƙirar Honda (EOD) da kuɗi N700,000.
Mataimakin ma’ajin jam’iyyar APC mai mulki na kasa, Dattuwa Ali Kumo ne ya ba shi kyautar, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin mutumin Gombe na zuwa Abuja
Shamsuddeen Ɗan Small ya ƙirƙiri tafiyar mai cike da kalubale daga Gombe zuwa Abuja, inda ya yi tafiyar kilomita kusan 548 akan keke.
A wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba, mai keken ya ce ya shirya wannan tafiya ne domin nuna goyon baya ga mataimakin ma’ajin APC saboda halayensa da ayyukan alherin da yake yi a Gombe.
Ya kuma yi kira ga Dattuwa da ya nemi takarar gwamnan jihar Gombe a 2027, inda ya ce yana da kyakykyawar damar siyasa da kuma halaye nagari.
An ba shi kyautar mota da kudi
Shugaban karamar hukumar Gombe, Imrana Haruna ne ya mika kyaututtukan mota da kuɗin ga Shamsuddeen Ɗan Small a madadin Dattuwa.
Ya ce Dattuwa ya ba mutumin wannan kyaututtuka ne domin jinjina masa bisa kasada da jajircewar da ya yi na nuna masa ƙauna da goyon baya.
Gombe za ta kawar da matsalar lantarki
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Gombe ta dauko aikin da zai kawo karshen matsalar wutar lantarki a jihar bayan Arewa ta fuskanci irin matsalar.
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya zai yi aiki da kamfanin China domin samar da tashar lantarki mai amfani da hasken rana.
Asali: Legit.ng